Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da wasu manyan daraktocin hukumar FIRS guda 9

Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da wasu manyan daraktocin hukumar FIRS guda 9

Yayin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yaki da barayin gwamnati da suka rike mukamai a gwamnatocin baya, sai gashi an samu wasu jami’an gwamnatin suna almundahana, wannan shine bonono an kulle da barawo.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wasu manyan jami’an hukumar tattara haraji ta kasa, watau FIRS, da suka kai mukamin daraktoci su Tara bisa wata bahallatsar biliyoyin nairori da suka tafka.

KU KARANTA: Naka naka ne: Yadda Buhari ya tarbi yayarsa a fadar shugaban kasa

Yaki da rashawa: EFCC ta cika hannu da wasu manyan daraktocin hukumar FIRS guda 9

Hukumar FIRS
Source: UGC

Daga manyan jami’ai na FIRS din da EFCC ta kama akwai Daraktan kudi da kididdiga na FIRS, Mohammed Auta, sai kuma wani daraktan da EFCC ke dakon dawowarsa daga kasar waje, inda aka ce ya tafi duba lafiyarsa, Peter Hena.

Majiyoyi sun tabbatar da cewar Hena ya kasance na hannun daman shugaban FIRS gaba daya, Babatunde Fowler, sai dai har yanzu babu wata takamaimen tabbacin ko shugaban FIRS Fowler nada hannu cikin bahallatsar.

Sai dai tabbataccen lamari shine EFCC ta kaddamar da zuzzurfan bincike akan badakalar sace naira biliyan shida da ta gano hannayen Mohamemd Auta, Peter Hena da wasu manyan daraktocin hukumar FIRS tsamo tsamo a ciki, kudin daya kamata ya tafi asusun gwamnati a matsayin haraji.

Haka zalika majiyarmu ta kara da cewa tun a ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumar take rike da wadannan daraktoci na hukumar tattara haraji ta kasa, FIRS, kuma a yanzu haka EFCC na fadada komarta don cafke duk wanda sunanshi ya fado a cikin wannan badakala ta cin amanar kasa.

Da majiyarmu ta tuntubi kaakakin hukumar EFCC, Orilade Tony akan batun, shima ya tabbatar da rahoton cafke manyan jami’an na hukumar FIRS, sai dai yace a dan bashi lokaci ya kammala samun bayanan da suka kamata kafin yayi manema labaru jawabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel