ASUU ta kalubalanci tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa ilimi a kasafin kudin kasa na bana

ASUU ta kalubalanci tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa ilimi a kasafin kudin kasa na bana

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana damuwa tare da rashin gamsuwar ta a kan tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa sashen ilimi cikin kasafin kudin kasa na bana.

ASUU a yayin bayyana rashin gamsuwar ta a kan tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa ilimi cikin kasafin kudin kasa na bana, ta kuma e gwamnatin ta yaudare ta sakamakon rashin tabbatar da yarjejeniyar da ta kulla tsakanin su a watan Fabrairun da ya gabata.

ASUU ta kalubalanci tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa ilimi a kasafin kudin kasa na bana

ASUU ta kalubalanci tanadin da gwamnatin tarayya ta yiwa ilimi a kasafin kudin kasa na bana
Source: UGC

Kawowa yanzu kamar yadda kungiyar ASUU ta bayyana, gwamnatin tarayya ba ta biya naira biliyan 25 na alawus din malaman jami'o'i da ta amince za ta biya gabanin janye yajin aikin ta watanni biyu da suka gabata.

Shugaban kungiyar ASUU reshen jami'ar Ibadan, Farfesa Deji Omole, shi ne ya bayar da shaidar hakan tare da bayyana damuwa akan rashin aminci da gwamnatin tarayya ta nuna musamman ta bangaren tanadin da ta yiwa sashen ilimi cikin kasafin kudin kasa na bana.

KARANTA KUMA: Atiku a take-taken sa zai kawo rudani da rashin zaman lafiya a Najeriya - Lauretta Onochie

Farfesa Omole ya ce gwamnatin tarayya ta angiza kungiyar ASUU wajen amincewa da alkawurran ta da a halin yanzu tanadin da ta yiwa sashen ilimi a Najeriya ya tabbatar da rashin amincin ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel