Yanzu-yanzu: Ranar Alhamis za'a yanke hukuncin karshe na Walter Onnoghen - CCT

Yanzu-yanzu: Ranar Alhamis za'a yanke hukuncin karshe na Walter Onnoghen - CCT

Kotun hukunta ma'aikatan gwamnati CCT ta ayyana ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu, 2019 matsayin ranar da za'a yanke hukunci kan tsohon Alkalin alkalai, Walter Onnoghen.

Alkalin kotun CCT, Danladi Umar, ya bayyana hakan ne bayan sauraron jawabin karshe daga bakin lauyoyin gwamnati da na Walter Onnoghen.

Gabanin yau, lauyan Onnoghen, Okon Nkanu Effiong, ya bukaci kotun tayi watsi da zarge-zargen ake yiwa tsohon Alkalain alkalan saboda babu gaskiya cikinsu kuma lauyoyin gwamnati sun gaza kawo isassun hujjoji.

Amma lauyan gwamnati, Aliyu Umar ya bukaci kotun tayi watsi da bukatar lauyan Onnoghen kuma ta kamashi da laifi.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano kudi $30,000 da wani babban lauya Joe Agi ya tura asusun bankin Jastis Walter Onnoghen, shugaban alkalan Najeriya da Buhari ya sallama.

Ya kara bayyana cewa Onnoghen bai bayyana wata asusun banki da ya mallaka a Heritage Bank ba, wani karin sabawa dokar Najeriya.

Dalilin hakan ya sa majalisar koli ta shari'a NJC ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawarar yiwa Walter Onnoghen ritayan dole amma kafin a faarga, Onnoghen ya aika wasikar murabus dinsa fadar shugaban kasa.

Har yanzu, fadar shugaban kasa bata ce uffin kan al'amarin murabus dinsa ba. Ana kyautata zaton cewa shugaba Buhari na sauraron sakamakon da zai fito daga kotun CCT ne kafin yayi magana ko ya dauki mataki kan Onnoghen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel