Boko Haram sun kai mamaya Chibok yayinda ake bikin shekara 5 da sace yan matan makarantar Chibok

Boko Haram sun kai mamaya Chibok yayinda ake bikin shekara 5 da sace yan matan makarantar Chibok

Yan ta’addan Boko Haram a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu, sun kai mamaya wani kauye a garin Chibok da ke jihar Borno, yayinda mamabobin kungiyar iyayen yan matan Chibok da aka sace ke bikin cika shekaru biyar da sace yaran nasu.

Daya daga cikin iyayen yaran ta fada ma jaridar Daily Trust cewa yayinda suke gudanar da lamuran tunawa da yaran a garin Chibok, labari ya iso garin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kai mamaya kauyen Kwarangullum sannan suna ta harbi ba kakkautawa.

Hakimin kauyen, Mallam Bulama, wanda ke a wajen garin, ma ya kira majiyar tamu sannan ya tabbatar da cewa yan ta’addan sun kai mammaya kauyen kuma suna ta barna a daren ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu.

Boko Haram sun kai mamaya Chibok yayinda ake bikin shekara 5 da sace yan matan makarantar Chibok

Boko Haram sun kai mamaya Chibok yayinda ake bikin shekara 5 da sace yan matan makarantar Chibok
Source: Twitter

Babu cikakken bayani akan adadin mutanen da suka rasa rayukansu, ko kuma irin barnar da yan ta’addan suka yi daga hukumomin tsaro da mazauna kauyen a yanzu haka.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Zamfara ta yaba ma gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan hakar ma’adinai

Idan za a tuna a ranar 14 ga watan Afrilu, 2014 ne yan ta’addan Boko Haram suka sace yan matan makarantar sakandare na Chibok su guda 276.

Wasu daga cikinsu sun tsere daga hannun yan ta’addan da kansu yayinda gwamnati ta tattauna aka saki wasu da dama daga cikinsu, amma dai har yanzu ba a ga sauran yan mata sama da dari ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel