Babu kafar tattaunawa da yan bindiga – Kwamishinan yan sandan Zamfara

Babu kafar tattaunawa da yan bindiga – Kwamishinan yan sandan Zamfara

- Rundunar yan sandan Najeriya ta kaddamar da cewar ba za ta bayar da kowani kafa na tattaunawa da yan bindiga ba a jiharZamfara

- A cewar yan sandan, yan bindigan su kwana da sanin cewa rundunar za ta tunkare su ne da karfinta

- Rundunar yan sandan ta kuma ba yan Najeriya tabbacin cewa kwanan nan yan fashi za su kare a jihar

Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara, Mista Celestine Okoye ya bayyana cewa jami’an tsaro a jihar ba za su tattauna da yan bindigan dake ta’addanci akan al’umman jihar ba.

Okoye ya bayyana matsayin ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu a Talata-Mafara yayinda yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan tattaunawa da kungiyar tsaro na jihar tayi.

Babu kafar tattaunawa da yan bindiga – Kwamishinan yan sandan Zamfara

Babu kafar tattaunawa da yan bindiga – Kwamishinan yan sandan Zamfara
Source: Facebook

“Idan ana maganar tattaunawa, yana nufin lamarin bai je da nisa ba. Mun rufe duk wata dama na tattaunawa.

“Yan bindigan su sani cewa zamu zo da karfinmu kuma babu batun tserewa gare su."

Yace, “Nan ba da dadewa ba, ayyukan yan bindiga zai kare a Zamfara, amman ba za mu bayyana jawabai ba akan hanyoyi da zamu bi don cimma nasara.”

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta jinjina wa gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan da suka shafi hake-haken ma’adinai a jihar, domin taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro da jihar ke fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya 23 na cikin jerin mutanen da za a yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya

Gwamna Abdul’aziz Yari ne yayi wannan yabawar a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu a Talata-Mafara bayan wata ganawa da shugabannin tsaro a jihar.

Yari ya bayyana cewa gwamnatin jihar na maraba da manufar gwamnatin tarayya, inda ya bayyana ta a matsayin abu mai kyau ga mutanen jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel