A sabon gwamnati, Ministoci daya ko biyu kawai zasu dawo – Majiya daga Aso rock

A sabon gwamnati, Ministoci daya ko biyu kawai zasu dawo – Majiya daga Aso rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara sabuwar gwamnatin shi da wani salo na sallamar duka ministoci amma zai bar daya ko biyu daga cikinsu, Majiya daga fadar shugaban kasa ya bayyana hakan.

Sabanin abinda ya faru a 2015 da ya dauke shi tsawon watanni shida kafin ya bayyana ministocin shi,wannan karan zai bayyana su a watan Yunin 2019.

Jaridar THIS DAY ta bayyana cewa shugaba Buhari yana takatsantsan akan zaben ministocin sa ne wanda zasu taimaka mai wajen wanzar da alkawuran da ya yiwa yan Nigeria.

Shugaban ya dau alkawarin cewa zai karfafa akan ribar da ya samu a karan shi na farko, musamman ta wajen aikin tsaro, cin hanci da rashawa da bunkasa tattalin arziki.

Ansha sukar Shugaba Buhari akan duk da cewa wasu daga cikin ministocinsa basa gudanar da aiyukan su yanda ya kamata, amma Shugaban ya zuba musu ido.

KU KARANTA: A baiwa ma'aikatanmu daman rike makamai - Hukumar FRSC

Daga bisani, Shugaban yayi la’akarin sallamar ministocin nashi a tsakiyar watan gobe dan samar da wasu sabbi.

Koda yake shugaban yana niyyar samar da sabbin ministocin,da yawa daga cikin ministocin suna yunkurin dawowa aiki.

“Ministoci sun bar aikin su, daga jin maganar Shugaban yasa suna guje guje akan su dawo dan kar abin ya shafe su." Wata majiya ta bayyana.

Yace Shugaban ya tattara sunayen wa’innan ministocin akan baza su dawo ba akaro na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel