Gwamnatin Zamfara ta yaba ma gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan hakar ma’adinai

Gwamnatin Zamfara ta yaba ma gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan hakar ma’adinai

- Gwamnatin jihar Zamfara ta jinjina wa gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan da suka shafi hake-haken ma’adinai a jihar

- Hakan na daga cikin kokarin da ake na kawo karshen matsalar rashin tsaro da ya addabi jihar

- Gwamna Abdul'aziz Yari ya bayyana cewa gwamnatin jihar na maraba da manufar gwamnatin tarayya domin abu ne mai kyau ga mutanen jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta jinjina wa gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan da suka shafi hake-haken ma’adinai a jihar, domin taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro da jihar ke fuskanta.

Gwamna Abdul’aziz Yari ne yayi wannan jinjinan a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu a Talata-Mafara bayan wata ganawa da shugabannin tsaro a jihar.

Yari ya bayyana cewa gwamnatin jihar na maraba da manufar gwamnatin tarayya, inda ya bayyana ta a matsayin abu mai kyau ga mutanen jihar.

Yari ya roki al’umman garuruwan jihar da su ba hukumomin tsaro hadin kai.

Gwamnatin Zamfara ta yaba ma gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan hakar ma’adinai

Gwamnatin Zamfara ta yaba ma gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan hakar ma’adinai
Source: UGC

A cewarsa, gwamnatin jihar na iya bakin kokarinta domin tabbatar da nasararsu.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya 23 na cikin jerin mutanen da za a yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya

Ya yaba ma gwamnatin tarayya kan tura hukumomin tsaro zuwa jihar sannan kuma “muna burin hakan zai kawo karshen ta’addanci a jihar nan."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamna Abdul'aziz Yari na jihar Zamfara, ya yi kira na neman rundunar dakarun sojin kasa da sauran hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen ci gaba da yakar 'yan baranda da masu tayar da zaune tsaye a fadin jihar.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Gwamna Yari ya yi wannan kira cikin wata sanarwa a ranar Lahadi da sanadin babban jami'in kula da harkokin sadarwa na gwamnatin sa, Mallam Bashir Kabir.

Mallam Kabir ya ce gwamna Yari ya yi kiran ne a yayin ganawa da kwamandan dakarun soji masu yaki da ta'addanci mai lakabin Sharan Daji, Manjo Janar Hakeem Otiki, cikin fadar gwamnatinsa da ke birnin Gusau a ranar Lahadi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel