A inganta harkar noma idan ana so a samu ayyukan yi –inji Sanusi II

A inganta harkar noma idan ana so a samu ayyukan yi –inji Sanusi II

Mai Martaba Sarki Muhammad Sanusi II na Kano yayi kira nu musamman ga gwamnatin tarayya da kuma na jihohi game da yadda za su rage rashin aikin da ake fama da shi a halin yanzu a Najeriya.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yayi kira ga gwamnatocin kasar nan suyi kokarin habaka harkar noma domin kawo karshen matsalar rashin sana’a. Sarkin yayi wannan jawabi ne wajen wani taro da aka yi a jigar Bauchi.

Sarkin Shanun Kano, Hassan Mohammed, shi ne wanda ya wakilci mai martaban wajen wannan taro da wata kungiya ta kwararrun Ma’aikatan Musulmai su ka shirya na shimfidar karatun tafsirin Al-Qur’ani na bana a Garin Bauchi.

KU KARANTA: Ma’aikata sun nemi Buhari yayi watsi da batun kara kudin fetur

A inganta harkar noma idan ana so a samu ayyukan yi –inji Sanusi II

Sarkin Kano ya bada shawarar a koma gona domin maganin rashin aikin yi
Source: Depositphotos

Mai Martaban ta bakin Sarkin Shanun na Kano, yake cewa an san Arewa ne da harkar noma, wanda shi ya rike kasar kafin a gano man fetur. Wannan ya sa Mai martaban yake gani idan aka rike gona, jama’a za su samu abubuwan yi.

Kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna, jama’a da dama sun halarci wannan lacca da aka shirya. Mai girma gwamnan jihar watau Mohammed Abubakar ya aika kwamsihinan sa na harkar addini domin ya wakilce sa a wannan zama.

Kwamishinan harkokin addinin musuluncin na jihar Bauchi, Alhaji Ado Sarkin Aska, yayi jawabi a madadin gwamna a taron, inda yayi kira ga wannan kungiya ta rika hada-kai da gwamnatin jihar domin ganin hakar ta, ta cin ma ruwa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel