Lamarin tsaro ya tabarbare – Dattawan Arewa

Lamarin tsaro ya tabarbare – Dattawan Arewa

Kungiyar dattawan arewa a jiya Lahadi, 14 ga watan Afrilu, sun nuna damuwa akan abunda suka kira da rushewar tsaro da kuma barazanar da rayuka da dukiyoyin mutane ke ciki a wasu yankunan Najeriya.

Jagoran kungiyar, Farfesa Abdullahi Ango ya fada wa manema labarai a Kaduna cewa lamarin yayi kamari sosai a yankin arewa, inda ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kula da mawyacin halin da mutanen yankin ke ciki.

A cewarsa, “yayinda har yanzu arewa ke karkashin barazanar Boko Haram, lamarin ya tabarbare da barazanar yan bindiga, sace-sacen mutane, fashi da makami, kungiyoyin matasa masu sace-sace, da kuma rikicin manoma da makiyaya.”

Lamarin tsaro ya tabarbare – Dattawan Arewa

Lamarin tsaro ya tabarbare – Dattawan Arewa
Source: Depositphotos

Yace yankuna da dama a arewa yanzu sun zama kasar yan fashi; yayinda harkar noma ke kan tafarkin lalacewa, inda ya kara da cewa dukkanin wadanan abubuwa na faruwa ne a wani yanki da aka yasar a tattalin arzikinta da mutanensta, musamman matasa.

KU KARANTA KUMA: Sanatocin PDP sun nuna adawar su ga Sanata Ahmad Lawan da APC ta tsaida a Majalisa

Abdullahi yayi gargadin cewa talauci da rashin ci gaba na iya haifar da zalunci da rikice-rikice a tsakanin al’umma.

Ya bayyana haramta hakar ma’adinai a Zamfara a matsayin ihu bayan hari.

Ya bayyana cewa hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ya dade yana wakana a yankunan kasar daban-daban sannan bai da nasaba da yawan tabarbarwar tsaro a arewa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel