Rundunar sojin Najeriya sun samu gagarumin nasara kan yan Boko Haram (Hotuna)

Rundunar sojin Najeriya sun samu gagarumin nasara kan yan Boko Haram (Hotuna)

Rudunar sojin Operation Lafiya Dole tare da hadin kan dakarun sojin kasar Chadi sun ragargaji da yan Boko Haram a wata arangama da sukayi a arewacin jihar Borno.

Kakakin hukumar sojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya sakin jawabin cewa rundunar sojin sun hallaka yan Boko Haram 27 kuma sun kwato manyan makamai da dama.

Jawabinsa yace:"Rudunar sojin Operation Lafiya Dole tare da hadin kan dakarun sojin kasar Chadi, a ranar 13 ga watan Afrilu 2019 sun yi artabu da yan Boko Haram a kauyukan Wulgo, Tumbuma, Chikun Gudu, da Bukar Maryam."

KU KARANTA: Takardar shaidar Firamare kadai mutum ke bukata domin takarar shugaban kasa - Babban Lauya

Rundunar sojin Najeriya sun samu gagarumin nasara kan yan Boko Haram (Hotuna)

Rundunar sojin Najeriya sun samu gagarumin nasara kan yan Boko Haram (Hotuna)
Source: Facebook

A yayinda wannan arangama, an hallaka yan Boko Haram 27 kuma an kwato wadannan makamai:

a. Motocin bindiga 5

b. Babura

c. Bindigar AK47 biyar

d. Bindigan Galile 1

e.Bindigan G3 1

f. Bindiga mai carbi 2

g. Bindigan baro jirage 2

h. Roka 4

i. Bindiga mai harba kanta 1

j. Bindigar M21 1

k. Bindigan gargajiya 1

l. Bam na roka 5

m. Harsasai 1000

n. Carbin harsasan AK47 biyar

o. Several Links of 12.7 MM

p. Mota kirar Land Cruiser Buffalo

q. Motar kirar Nissan GT

r.Lalataciyyar Land Criuser 1

s. Tuta da injin nika 1

Ba bu wani jami'an sojan Najeriya ko Chadi da ya rasa rayuwarsa.

Kana ana gudanar da sintiri musamman a lungunan Gamboru-Ngala domin lallasan yan ta'addan masu guduwa daga harin da jami'an sojin MNJTF ke kai musu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel