Chibok: Sai tarin alkawari babu cikawa – Iyaye sun fadawa Buhari

Chibok: Sai tarin alkawari babu cikawa – Iyaye sun fadawa Buhari

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust ta jiya Lahadi 14 ga Watan Afrilun 2019 cewa wasu tarin Iyayen yaran nan na Garin Chibok da aka sace shekaru 5 da su ka wuce sun koka da halin da su ke ciki.

Jaridar kasar ta rahoto cewa Iyayen wadannan yara da aka sace tun ba yau ba, sun bayyana cewa sun gaji da tarin alkawarin da shugaban kasar yake yi masu na cewa zai ceto ragowar yaran da su ka rage a hannun ‘Yan Boko Haram.

Shugaban kungiyar Jire Dole Network, Hamsatu Allamin, ita ce tayi wannan jawabi a Ranar Lahadin nan da ta gabata inda tace shekara da shekaru kenan gwamnatin Najeriya tana yi wa Iyayen wannan ‘Yan mata alkawura na iska.

KU KARANTA: Ina nan da maganar Yaran Chibok a rai na har gobe - Buhari

Hamsatu Allamin tayi wannan jawabi ne a cikin Garin Maiduguri na jihar Borno a taron da aka shirya domin tunawa da Yaran makarantar Chibok da aka sace tun a Afrilun 2014, wanda har yau ba a san inda fiye da 100 daga cikin su ke ciki ba.

Allamin ta nemi gwamnatin kasar tayi bakin kokarin ta na ganin an kawo karshen satar kananan yara da ‘yan mata, sannan kuma Jagorar kungiyar ta Jire Dole Network tana so shugaba Buhari ya gano sauran yaran da ke hannun Boko Haram.

Shekaru 5 kenan da dauke wadannan yara a makaranta, wannan ne ma ya sa Iyayensu ke nuna shakkar cewa za a taba kubutar da ragowar yaran da su ka makale a hannun 'Yan Boko Haram. Hamsatu Allamin tace dole sai gwamnati ta tashi tsaye.

KU KARANTA: Yadda aka saki wasu 'Yan Matan Chibok kwanakin baya

Hajiya Hamsatu Allamin ta kuma koka da yadda aka kai wa wasu mata farmaki a lokacin da ‘yan ta’adda su ka kai wa tawagar gwamnan Borno hari kwanaki a Garin Dikwa da Ngala. Allamin take cewa wannan abu yana yi wa Matan jihar mugun ciwo.

Ayuba Alamson wanda tana cikin wadanda aka sace Yarinyarta, tace gwamnatin APC ta manta da labarin Yaran na Chibok 112 da ke tsare har gobe. Alamson tace yanzu APC tayi watsi da batun ceto yaran bayan darewar ta a kan mulki.

Alamson tace Iyayen wadannan yara akalla 18 ne su ka mutu a dalilin ciwon dauke ‘Ya ‘yan cikin su da aka yi. Wannan Baiwar Allah tace ya zama dole shugaba Buhari ya ceto ragowar ‘yan matan ya daina yi masu alkawarin bogi maras tasiri.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel