Yansanda sun samu gagarumar nasara akan yan bindigan hanyar Kaduna-Abuja

Yansanda sun samu gagarumar nasara akan yan bindigan hanyar Kaduna-Abuja

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da wata gagarumar nasara data samu a jahar Kaduna, inda jami’anta suka bindige wasu gagararrun yan fashi da makami su Tara dake addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Frank Mba ya bayyana haka a ranar Lahadi, inda yace sun halaka yan bindigan a wani samame da suka kaddamar a dajin Akilbu dake gefen babbar hanyar.

KU KARANTA: Shugabancin majalisa ta 9: An bayyana Sanatan da gwamnonin APC 24 ke muradi

Dansanda Mba yace wannan lamari ya auku ne a ranar 10 ga watan Afrilu, inda aka yi zazzafar musayar wuta tsakanin jami’an Yansanda da yan bindigan, amma Yansanda suka nuna jarumta, kwarewa da sanin makaman aiki har suka samu nasara akansu.

Kaakakin ya kara da cewa sun samu nasarar kwace bindigu kirar AK 47 guda shida da wata bindiga kirar Pump Action, alburusai guda dubu daya da dari biyu da shida, da sauran muggan makamai da yan fashi ke amfani dasu.

Sai dai kaakakin yace Dansanda guda daya ya samu rauni, kuma tuni aka garzaya dashi asibiti inda a yanzu haka yake samun kyakkyawar kulawar data kamata, sa’annan yace sun bin sawun wasu yayan kungiyar yan fashin guda biyu da suka tsere.

Daga karshe Frank Mba ya bayyana jin dadinsa da aikin da rundunar Yansanda ta musamman ta ‘Puff Adder’ ke gudanarwa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda yace ya gamsu da nasarar da suke samu akan yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel