Sanatocin PDP sun nuna adawar su ga Sanata Ahmad Lawan da APC ta tsaida a Majalisa

Sanatocin PDP sun nuna adawar su ga Sanata Ahmad Lawan da APC ta tsaida a Majalisa

Wasu sababbin Sanatoci na jam’iyyar adawa ta PDP sun fara nuna cewa fau-fau ba za su goyi bayan takarar Sanata Ahmad Lawan a zaben majalisar dattawa da za ayi nan da watanni 2 masu zuwa ba.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sanata Enyinnaya Abaribe da kuma Gabriel Suswam, sun tabbatar da cewa sam ba su tare da Ahmad Lawan. Sanatocin a mabanbantan hirar da su kayi sun bayyana dalilin kin goyon bayan Lawan.

Wadannan ‘Yan majalisu sun bayyana cewa ba za su so su zabi shugaban da zai zama ‘dan amshin shatar fadar shugaban kasa ba, wanda kurum zai rika yin duk abin shugaban kasa yace ba tare da yin la’akari da ‘Yan majalisa ba.

‘Yan majalisun PDP sun nuna cewa za su taru su marawa duk wani Sanatan jam’iyyar APC da ake tunani ba zai rika taka rawar masu rike da madafan iko a majalisar ba. Sanatocin na ganin hakan zai sa ‘yan majalisar su ci gashin-kan su.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisan Najeriya sun raba Biliyan 140 a shekara guda

Sanatocin PDP sun nuna adawar su ga Sanata Ahmad Lawan da APC ta tsaida a Majalisa

Sanatocin PDP su na gudun ‘Dan kanzagin Buhari a Majalisa
Source: UGC

Wani daga cikin Sanatocin jam’iyyar hamayyar kasar yake cewa ganin yadda jam’iyyar APC mai mulki ta zakulo Ahmad Lawan tace dole sai ya zama shugaban majalisar dattawan kasar, zai yi kokarin taka majalisar domin ya burge APC.

Majiyar take cewa wani sabon Sanata da aka zaba a PDP ya bayyana cewa hankalin su ya fi kwanciya da tsohon gwamnan jihar Gombe watau Danjuma Goje da kuma tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan kasar Ali Ndume.

Sanatan yace duk da sun san cewa Sanata Ndume, ‘Dan-a-mutun shugaba Buhari ne, amma da alamu cewa za su iya aiki da shi. Sabon Sanata George Akume yace APC za ta sha mamaki domin kuwa sam ba za su marawa Lawan baya ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel