Shugabancin majalisa ta 9: An bayyana Sanatan da gwamnonin APC 24 ke muradi

Shugabancin majalisa ta 9: An bayyana Sanatan da gwamnonin APC 24 ke muradi

Gwamnan jahar Borno, kuma shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya, Gwamna Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnonin da suka lashe zaben shiga majalisar dattawa a matsayin Sanatoci sun amince da takarar Sanata Ahmad Lawan a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kashim ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga bakin manema labaru a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi, inda yace haka zalika gwamnonin kuma sun amince da Femi Gbajabiamila a matsayin wanda zai dare kujerar kaakakin majalisar wakilai.

KU KARANTA: Tsautsayi baya wuce ranarsa: Ruwa ya cinye wani karamin yaro a jahar Kano

Gwamna Kashim ya kara da cewa gaba daya kafatanin zababbun Sanatocin jahar Borno da ma yan majalisun dake wakiltar jahar Borno a majalisar wakilai sun yarda, sun amince da zaben Sanata Ahmad Lawan da Gbajabiamila a matsayin shuwagabannin majalisar dokoki ta tara.

A cewar gwamnan, hanya daya tilo da gwamnonin APC zasu sakanya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari duba da irin goyon bayan da suka samu daga gareshi shine ta hanyar yin biyayya ga umarninsa a siyasance, tare mara ma muradun gwamnatinsa baya.

“Kafatanin gwamnonin APC, har ma da wadanda suka zamto zababbun Sanatoci sun yi amanna da matsayin uwar jam’iyya game zaben shuwagabannin majalisun dokokin, dari bisa dari, don haka muma a jahar Borno mun yi biyayya ga bukatar jam’iyyarmu data shugaban kasa.

“Idan akace a kyale kowa ya zabi abinda ya ga dama, toh lallai za’a samu barakar da za tayi wuyan dinkewa, don haka ya zama wajibi a garemu mu hada kai da bukatar shugaban kasa.” Inji shi.

Gwamnan na cikin tawagar da ta raka shugaba Buhari zuwa kasar Chadi da nufin tattauna hanyoyin magance tsaro, musamman a yankin tafkin Chadi ne, inda ya jinjina ma Buhari game da kokarin da yake na kawo zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel