Tallafin man fetur: Kar Gwamnatin Tarayya ta biyewa IMF – Inji NLC

Tallafin man fetur: Kar Gwamnatin Tarayya ta biyewa IMF – Inji NLC

Mun samu labari cewa Kungiyar NLC ta ‘Yan kwadagon Najeriya ta ja kunnen Gwamnatin Tarayya da ta guje daukar shawarar da hukumar bada lamuni ta Duniya watau IMF ta bata kwanan nan.

Hukumar ta IMF ta Duniya tayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta cire tallafin man fetur din da ta ke daukar nauyi a halin yanzu. IMF tana ganin wannan zai bunkasa tattalin kasar yayin da ita kungiyar NLC ta ke ganin ba haka ba.

Kungiyar ta ma’aikatan kasar tace idan har gwamnatin kasar ta biyewa wannan shawara, za a samu karin farashin man fetur, wanda a karshen mutanen Najeriya za su shiga cikin wani mawuyacin hali a sakamakon wannan mataki.

NLC tayi wannan bayani ne ta bakin shugabanta na kasa watau Kwamared Ayuba Wabba wanda yayi jawabi wajen wani babban taro na musamman da kungiyar kwadagon kasar ta shirya a babban birnin tarayya Abuja kwanan nan.

Tallafin man fetur: Kar Gwamnatin Tarayya ta biyewa IMF – Inji NLC

Ayuba Wabba ya caccaki IMF mai bada lamuni a Duniya
Source: Depositphotos

Ayuba Wabba yake cewa a duk lokacin da IMF mai bada lamuni tayi magana a kan Najeriya, babu abin da ta ke kira sai a cire tallafin fetur, a nakasa darajar Naira, sannann kuma yunkurin kawo yadda za a kashe kasuwancin a Najeriya.

Wabba ya kuma soki tsarin da ake bi wajen biyan tallafin fetur a yanzu inda yayi kira ga gwamnati da ta gyara matatun kasar da ake da su. Shugaban na NLC ya kuma koka da yadda aka dogara da fetur kacokam domin samun kudi.

NLC dai ta shirya wannan taro ne kamar yadda ta saba domin tunawa da mutanen kasar Cuba da irin wahalar da su ka sha a Duniya. NLC ta na goyon bayan kasar ne saboda nasabar ta da Nahiyar Afrika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel