Kisan gilla: Yaron jigon jam’iyyar PDP ya sha wuta a hannun yan bindiga

Kisan gilla: Yaron jigon jam’iyyar PDP ya sha wuta a hannun yan bindiga

Wasu gungun yan bindiga sun halaka guda daga cikin yayan wani kusa a jam’iyyar PDP ta kasa, Prince Yandev Amaabai, a karamar hukumar Gboko ta jahar Benuwe, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun bindige yaron mai suna Orkuma Yndev Amaabai ne a daren Asabar, 13 ga watan Afrirul yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, inda suka bi sawunsa a baya, suka dirka masa harsashi.

KU KARANTA: Tsautsayi baya wuce ranarsa: Ruwa ya cinye wani karamin yaro a jahar Kano

Sai dai mutanen da suka san yaron, suka kuma san mahaifinsa sun danganta lamarin da aikin abokan hamayyar babannasa a siyasance, inda suka zargesu da halaka yaron don aika ma mahaifinsa sako, amma dai Yansanda sun musanta hakan, inda suka ce bincike ne kadai zai iya tabbatar da hakan.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Benuwe, Catherine Anene ce ta tabbatar da kisan, sa’annan ta bayyana cewa jami’an rundunar Yansanda na tsaye kyam don tabbatar da cikakken bincike game da lamarin.

Zuwa yanzu dai an mika gawar mamacin a dakin ajiyan gawarwaki dake wani babban asibitin garin Gboko don jiran kammala shirye shiryen binneshi kamar yadda al’adansu ta tanadar.

Ga masu bibiyan al’amuran dake faruwa a jahar Benuwe zasu fahimci cewa an dade ana samun hare haren yan bindiga a jahar, wanda wasu ke dangantawa ga ayyukan makiyaya da kuma matasa zauna gari banza na jahar.

Domin kuwa ko a daren Talata 20 ga watan Maris sai da yan bindiga suka kai wani mummunan hari a kauyen Tser Uoreleegeb dake cikin mazabar Ubabai na karamar hukumar Guma, inda suka kashe akalla mutane goma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel