Katafaren gidan Diezani Madueke da ke Fatakwal ya zama mallakar Najeriya

Katafaren gidan Diezani Madueke da ke Fatakwal ya zama mallakar Najeriya

Mun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya, tayi nasarar samun damar karbe wasu kadarorin da tsohuwar Ministar man fetur na Najeriya ta mallaka.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust a farkon makon nan, EFCC ta reshen shiyyar Legas ta sa an yi ram da wasu dukiyoyi na Diezani Alison-Madueke, da kuma wani mutumi Donald Chidi Amangbo.

Rahotanni sun nuna cewa kamfanin Sequoyah Properties Limited yana cikin wanda yayi asarar dukiyoyinsa wajen EFCC. Daga cikin kadarorin da hukumar ta sa aka karbe akwai wani makeken gida a kudancin Najeriya.

An bada adireshin wannan gida ne da titin Nnmadi Azikiwe na Unguwar GRA a cikin Garin Fatakwal na jihar Ribas. Ana tunani tsohuwar Ministar mai, ita ce ta mallaki wannan katafaren gida da yanzu gwamnati ta karba.

KU KARANTA: Kotu ta yankewa wasu Matasa hukuncin dauri a gidan kaso

Katafaren gidan Diezani Madueke da ke Fatakwal ya zama mallakar Najeriya

Kotu ta karbe wasu wano gida na Diezani Alison-Madueke
Source: Depositphotos

Babban Kotun tarayya da ke zama a Legas ne ya bada damar karbe wadanan dukiyoyi na Ministar da wasun ta a wata shari’a da Alkali Chuka Obiozor yayi. Yanzu gidan na Diezani Madueke ya koma hannun gwamnati.

Mai shari’a Chuka Obiozor ya bada damar hukuma ta some rike wannan kadarori kafin a kammala binciken da za ayi. Kotu tana zargin cewa an mallaki wannan gida ne ta hanyar da ba ta dace ba, don haka ta karbe ikon sa.

Yanzu dai Alkali Obiozor ya umarci EFCC da ta bayyanawa Duniya wannan hukunci da aka dauka domin masu neman daukaka kara su dumfari kotu. Ana sa rai dai za a yanke hukuncin karshe game da gidan a Watan Mayu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel