APC ta sahalewa Lawan neman goyon bayan mambobi da gwamnonin PDP

APC ta sahalewa Lawan neman goyon bayan mambobi da gwamnonin PDP

Jam'iyyar APC mai mulki ta ce tayi maraba da yunkurin 'ya'yanta na neman goyon bayan mambobin jam'iyyar adawa a takarar neman shugabancin majalisa da suke yi.

A wani jawabi da ta fitar a ranar Lahadi, APC ta ce yin hakan ba laifi ba ne, a saboda haka bai ci karo da dokar jam'iyya ba.

"Mun samu korafe-korafen cewar 'ya'yan jam'iyyar mu na gana wa da mambobin jam'iyyar adawa a kan siyasar cikin zauren majalisa. Muna son jama'a su san cewar jam'iyyar mu ba ta damuwa a kan irin wadannan gana wa ko tattauna wa. Siyasa, a ko ina cikin fadin duniya, ta gaji haka. Sannan mu na masu yin watsi da wasu rahotanni a kafafen yada labarai da ke bayyana cewar mambobin da suka yi hakan sun saba wa jam'iyya. Jam'iyyar APC ke da rinjaye a dukkan zauren majalisar kasa, a saboda mu na da yawan da zamu samar da shugabancin majalisa," kamar yadda ya ke a cikin jawabin da Lanre Issa-Onilu, sakataren yada labaran jam'iyyar APC, ya sanya wa hannu.

Jawabin na zuwa ne a matsayin martanin jam'iyyar APC a kan ganawar Sanata Ahmed Lawan, dan takarar shugabancin majalisa da fatar shugaban kasa ke goyon baya, da wasu mambobi da shugabannin jam'iyyar PDP. Za a yi zaben shugabannin majalisun tarayya a watan Yuni.

APC ta sahalewa Lawan neman goyon bayan mambobi da gwamnonin PDP

Lawan da Gbajabiamila
Source: Twitter

Babban kalubalen da Lawan ke fuskanta shine daga mambobin da aka zaba a karkashin jam'iyyarsa ta APC, wadanda sanatan jihar Borno, Ali Ndume, ke jagoranta.

A cewar wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, sanata Lawan ya gana da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP uku domin karfafa takarar da ya ke yi ta neman zama shugaban majalisar dattijai.

Kazalika, Femi Gbajabiamila, dan takarar APC a kujerar majalisar wakilai, na cigaba da gana wa da mambobin jam'iyyar PDP domin neman goyon bayansu.

DUBA WANNAN: Tuna baya: Abubuwan da Sa'adu Zungur ya fada a kan makomar arewa shekaru 61 da suka wuce

Batun gana wa da mambobin jam'iyyar adawar ya jawo cece-kuce ne saboda ya saba da matakin da shugaban jam'iyyar APC, Adams Ohiomhole, ya bayyana da farko.

Oshimhole, yayin gana wa da sabbin mambobin majalisar tarayya da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC a watan Maris, ya cika bakin cewar sune ke da rinjaye, a saboda haka ba zasu bar wa jam'iyyar PDP kowacce kujera ba, bayan ta shugaban marasa rinjaye, a jerin kujerun shugabannin jam'iyya.

Ya yi gargadi a kan hada kai tare da su, saboda abinda ya faru a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel