Babu batun janye tallafin man fetur a yanzu, inji Ministar Kudi

Babu batun janye tallafin man fetur a yanzu, inji Ministar Kudi

-Ba mu da bukatar janye tallafin man fetur a halin yanzu, zance daga bakin Zainab Ahmed

-Akwai bukatar mu nemi mafita kafin tunanin aiwatar da wannan yinkuri na janye tallafin mai inji Ministar kudi

Gwamnatin tarayya ta sake bayyana kudurinta dangane da janyen tallafin man fetur inda tace ba ta da niyyar yin hakan a nan kusa.

Ministar kudi, Zainab Ahmed ce tayi wannan furuci a ranar Lahadi yayinda take tsokaci akan taron da ya gudana na hadaka tsakanin Kungiyar kudi ta duniya wato ‘IMF’ da kuma Bankin duniya a babban birnin Amurka, Washington DC.

Ministar tayi magana akan shawarar da IMF ta baiwa Najeriya kan cewa a janye tallafin na man fetur inda tace hakan ka iya jefa kasar nan cikin halin tsaka mai wuya musamman fannin cinikin man.

Zainab Ahmed

Zainab Ahmed
Source: UGC

KU KARANTA:Dalilin da yasa baza a iya kawar da sayen kuri’a ba, inji Farfesa Munzali

“Babu wani shiri na janye tallafin man a halin yanzu, duk da shawarar da Kungiyar kula da kudi ta duniya ta bayar na da matukar amfani, amma sai dai idan muka bi shawarar tasu muka janye tallafin bamu san wane hali kasarmu zata shiga ba a yanzu. Saboda haka babu maganar janye tallafin man a yanzu.”

“Zamu dukufa wajen cigaba da aiki da kwararru domin samun mafita akan janye tallafin musamman idan janye shi ya zamo dole. Domin haryanzu bamu cinma matsayar janye tallafin ba. Ta sake cewa, hakika taron da akayi a birnin Washington DC ya kayatar kwarai da gaske wanda ya baiwa Najeriya dama domin bayyana matsalolin da take fuskanta a fannin tattalin arziki da kuma hanyoyin da ake bi domin magance su.

“A matsayina na daya daga cikin masu wakiltar kasashen Afirka ashirin da uku, na fuskanci taron inda nayi kira akan a daidaita harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe ba tare da nuna son kai ba daga wadansu bangarori. Har wa yau, na sake janyo hakalin Bankin Duniya akan irin kalubalen da muke fuskanta wajen kaddamar da ayukan cigaban muhalli da kuma al’amuran yau da kullum wanda sanadiyar hakan muke samun cikas wurin gina ababen cigaban kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel