Bukola Saraki ya aika ta’aziyyar Marigayi Galadima Mamman Nasir

Bukola Saraki ya aika ta’aziyyar Marigayi Galadima Mamman Nasir

Mun ji labari cewa Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Dr. Bukola Saraki, yayi magana bayan rasuwar daya daga cikin manyan Dattawan Arewacin Najeriya watau Alkali Mai shari’a Mamman Nasir.

Bukola Saraki ya nuna takaicinsa na rashin Galadiman Katsina, Mamman Nasir, da aka yi a cikin karshen makon nan. Shugaban majalisar tarayyan ya aika sakon ta’aziyyar sa ne ta hannun Hadiminsa Yusuph Olaniyonu.

Dr. Bukola Saraki yake cewa Marigayin ya kasance babban Alkali maras tsoro a wajen aiki a lokacin da yake raye. Shugaban majalisar ya kara da cewa Alkali Mamman Nasir mutum ne mai tsayin daka da kuma kishin kasa.

Bukola Saraki ya aika ta’aziyyar Marigayi Galadima Mamman Nasir

Bukola Saraki ya ji takaicin rasuwar Mai shari'a Mamman Nasir
Source: Twitter

A jawabin ta’aziyyar babban Sanatan kasar, yace Marigayin yana cikin wadanda su ka taimaka wajen gyara harkar shari’a a Najeriya. Alkali Mamman Nasir ya rike shugaban kotun daukaka kara na sama da shekaru 10 a kasar nan.

Tsohon gwamnan yake cewa ba da dadewa bane ya hadu da tsohon Alkalin wajen taron Lauyoyi, har ya mika masa lambar yabo da jinjina. Saraki yace a wancan lokaci bai taba kawo cewa Mamman Nasir yana daf da barin Duniya ba.

A karshe Saraki yayi wa Mamacin addu’a inda ya roki Ubangiji Allah da ya saka sa a cikin mafificiyar Aljanna ta Firdausi tare da kuma rokon Allah ya ba Iyalin Marigayin hakurin jure wannan rashi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel