Akwai bukatar Buhari ya maida hankali akan kashe-kashen dake faruwa a Arewa, inji Dattawan Arewa

Akwai bukatar Buhari ya maida hankali akan kashe-kashen dake faruwa a Arewa, inji Dattawan Arewa

-Yakamata ace an shawo kan matsalar rashin tsaron da ta addabi arewacin Najeriya

-An dauki tsawon lokaci arewacin kasar nan na cikin damuwa ta rashin tsaro wanda ke sanadiyar rashin rayuka kai har ma da dukiyoyi

Kungiyar Dattawan Arewa ta nuna matukar bacin ranta akan tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya kana tayi kira ga Shugaba Buhari da ya nuna damuwa da kuma tausayi ga mutanen wannan yankin.

Da take zantawa da manema labarai, Kungiyar wacce shugabansu Farfesa Ango Abdullahi yayi magana a madadinsu yace, kungiyar tasu na cike da bakin ciki bisa ga tabarbarewar tsaro dake addabar bangarorin kasar nan, musamman jihohin Arewa, yayinda hakan ke sanadiyar rasa rayuka da kuma dukiyoyi.

Farfesa Ango Abdullahi

Farfesa Ango Abdullahi
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN:Ku daina bin masu laifi a guje, Hukamar kare hadurra ta kasa (FRSC) ta gargadi jami’anta ugu da kari, ya sake cewa

“Mu baza mu taba sanya ido akan irin wadannan kashe-kashe da ke faruwa a yankinmu na Arewa da ma kasa baki daya ba. Mun kasance cikin wasu yan shekaru yanzu haka muna rayuwa cikin rashin zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali wanda a halin yanzu yakamata ace hakan ya kau.

“Sam bai kyautu ba daga wurinmu idan muka ce zamuyi shiru mu ki jawo hankalin Shugaba Buhari domin ya dauki matakin da ya dace akan wannan lamari da yake addabar arewacin kasar nan na tsawon lokaci zuwa yanzu.

“Kungiyarmu ba zata ki fadan gaskiyar lamari ba akan koma wane irin abune yake faruwa, saboda mu ba wai muna tare da wannan jam’iyar bane ko waccan, a dalilin haka ko wace jam’iya ke mulki ya zama wajibi mu fada mata gaskiya akan al’amuran kasar nan.”

A dai dai lokacin da kasar nan ke fama da rikicin Boko haram, kana kuma yanzu akwai wasu matsaloli na daban bangaren tsaro wadanda suka hada da rikicin manoma da makiyaya, garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin kabila da dai sauransu. Mun fahimci cewa yawan wadannan ta’adaccin na aukuwa ne a arewacin Najeriya wanda hakan ke kawo da cikas ga harkokin noma.

Kungiyar ta kara da cewa, wannan lamari ya samu asaline saboda rashin kulawa da mutanen wannan yankin musamman matasan cikinsu. A mafi yawanci lokuta rashin aikin yi ga matasa kan iya haifar da shigar wasun su cikin irin wannan ta’addanci.

“A karshe muna kira ga Shugaba Buhari da yayi amfani da kwarewarsa da kuma fasaharsa ta mulki wajen kawo karshe wannan kashe-kashen dake ci mana tuwo a kwarya a yankinmu na arewancin kasar nan musamman a jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Binuwai, Neja, Filato, Taraba da ma sauran jihohin arewacin kasar.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel