Yadda 'Yan Majalisa su ka kashe Naira Biliyan 140 a 2018

Yadda 'Yan Majalisa su ka kashe Naira Biliyan 140 a 2018

Idan ba ku manta ba, a karshen makon jiya ne shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bada umarnin cewa a bayyanawa Duniya abin da majalisar tarayya ta kashe a kasafin kudin shekarar 2018.

Kundin kasafin kudin majalisar da aka fitar mai shafi kusan 45 ya nuna cewa ‘yan majalisar wakilan tarayya da kuma majalisar dattawa sun kashe kusan Naira Biliyan 140 daga kasafin kudin kasar nan a shekarar da ta gabata.

Mun kawo maku diddikin yadda aka batar da wannan kudi kamar yadda takardun majalisar su ka nuna:

An warewa majalisa N139, 500, 000, 000 a 2018, wanda daga ciki Naira Biliyan 35.5 su ka tafi wajen Sanatocin kasar. Daga cikin wannan kudi kuma, Naira Biliyan 57.4 ne su ka tafi zuwa asusun takwaran su da ke majalisar wakilai.

KU KARANTA: Sanata ya fasa kwan yadda PDP ke neman karbe Majalisa

Kasafin na bara ya nuna cewa an fitar da Naira Biliyan 10.2 domin biyan albashin Hadimai da manyan mukarraban ‘yan majalisun tarayyar kasar. Wadandan ma’aikata su ne ke bada shawarwari kuma su ke taimakawa ‘yan majalisar.

Har wa yau, an ware sama da Biliyan 15 a matsayin kudin ma’aikatan majalisa wadanda ke aikin zaman kan-su. Hukumar da ke kula da harkar aikin ‘yan majalisa a kasar kuma ta samu fiye da Naira Biliyan 2.7 daga wannan tarin kudi.

A karshe mun fahimci cewa an fitar da wasu kudi da su ka haura Naira Biliyan guda domin wasu aikace-aikacen ‘yan majalisar. Haka kuma ragowar kusan Naira Biliyan 4.4 sun tafi ne ga wata ma’aikatar koyon aikin majalisa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel