Za mu tallafa wajen yakar ta'addanci a jihar Zamfara - Gwamna Yari ya shaidawa hukumomin tsaro

Za mu tallafa wajen yakar ta'addanci a jihar Zamfara - Gwamna Yari ya shaidawa hukumomin tsaro

Gwamna Abdul'aziz Yari na jihar Zamfara, ya yi kira na neman rundunar dakarun sojin kasa da sauran hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen ci gaba da yakar 'yan baranda da masu tayar da zaune tsaye a fadin jihar.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Gwamna Yari ya yi wannan kira cikin wata sanarwa a ranar Lahadi da sanadin babban jami'in kula da harkokin sadarwa na gwamnatin sa, Mallam Bashir Kabir.

Gwamnan jihar Zamfara; Abdul'aziz Yari

Gwamnan jihar Zamfara; Abdul'aziz Yari
Source: Depositphotos

Mallam Kabir ya ce gwamna Yari ya yi kiran ne a yayin ganawa da kwamandan dakarun soji masu yaki da ta'addanci mai lakabin Sharan Daji, Manjo Janar Hakeem Otiki, cikin fadar gwamnatin sa da ke birnin Gusau a ranar Lahadi.

Jami'in sadarwa na gwamnatin jiar Gusau ya bayyana yadda gwamna Yari ya jinjina tare da yabawa rundunar dakarun sojin kasa da kuma sauran hukumomin tsaro wajen tsayuwar daka ta ci gaba da yakar miyagun ababe masu tayar da zaune a jihar Zamfara da kewayen ta.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun hallaka 'yan fashi da makami 9 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Gwamna Yari ya bayyana rashin dadin sa matuka kan yadda ta'addanci ya salwantar da rayukan Mutane gami da asarar dukiya mai tarin yawa a jihar Zamfara musamman a sanadiyar satar shanu da kuma garkuwa da mutane.

Gwamnan ya bayar da tabbacin sa na tallafawa dukkanin hukumomin tsaro a yayin da suke fafutikar dawo da martabar da wanzar da aminci na zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel