Yanzunnan: Rundunar sojin sama ta kaiwa 'yan ta'adda hari a dajin Kagara, Zamfara

Yanzunnan: Rundunar sojin sama ta kaiwa 'yan ta'adda hari a dajin Kagara, Zamfara

- Rundunar sojin sama da ke atisayen DIRAR MIKIYA, ta kai wani hari tare da lalata manyan dakunan ajiye kayayyakin 'yan ta'adda a dajin Kagara da ke Zamfara

- Rahotanni sun tabbatar da cewa an lalata mabuyar 'yan ta'addan, kuma har an kashe 'yan ta'adda hudu a harin

- Rundunar sojin sama tare da hadin guiwar sauran jami'an tsaro za su yi duk mai yiyuwa domin kakkabe dukkanin 'yan ta'adda a Arewa maso Yammacin kasar

A ci gaba da amfani da jiragen yakinta na sama domin kakkabe dukkanin mabuyar 'yan ta'adda a Zamfara da makwabtanta, Rundunar sojin sama da ke atisayen DIRAR MIKIYA, ta kai wani hari tare da lalata manyan dakunan ajiye kayayyakin 'yan ta'adda a dajin Kagara da ke jihar Zamfara.

Rundunar ta kai wannan harin ne a ranar 13 ga watan Afrelu, 2019, bayan da ta samu kwararan rahotanni kan cewar sauran 'yan ta'addar da suka rage a dajin sun kwashe kayayyakinsu da suka hada da fetur, ababen hawa da makamai zuwa wasu dakunan ajiya daban, bayan da suka sha lugudan wuta a kwanakin nan.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar sojin saman, Air Commodore Ibikunle Daramola, inda ya bayyana cewa rundunar ta tura jirginta na yaki mai kirar Mi-35 tare da na'urar ganin kwakwaf wacce ta taimaka wajen kai harin.

KARANTA WANNAN: 'Matakan da ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen matsalar man fetur'

Yanzunnan: Rundunar sojin sama ta kaiwa 'yan ta'adda hari a dajin Kagara, Zamfara

Yanzunnan: Rundunar sojin sama ta kaiwa 'yan ta'adda hari a dajin Kagara, Zamfara
Source: Facebook

Ya ce a lokacin da jirgin ya isa wajen, babu alamar akwai wani abu mai motsi, amma da jirgin ya matsa kasa sosai, an hangi wasu daga cikin 'yan ta'addan suna fitowa daga mabuyarsu domin neman tsira da rayukansu.

"Jirgin ya kaddamar da harin, kuma ya samu nasarar lalata mabuyar 'yan ta'addan da ma'ajiyarsu. Wasu daga cikin 'yan ta'addan da suka yi yunkurin mayar da martanin harbi ga jirgin, sun gamu da ajalinsu bayan da jirgin ya kakkabe su.

"Rahotanni daga majiya mai tushe da suka had'a da mazauna kusa da yankin sun tabbatar da cewa an lalata mabuyar 'yan ta'addan, kuma har an kashe 'yan ta'adda hudu a harin," a cewar Daramola.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar sojin sama tare da hadin guiwar sauran jami'an tsaro za su yi duk mai yiyuwa domin kakkabe dukkanin 'yan ta'adda daga shiyyar Arewa maso Yammacin kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel