Muna da isasshen man fetur - Kachikwu ya tabbatarwa 'yan Nigeria

Muna da isasshen man fetur - Kachikwu ya tabbatarwa 'yan Nigeria

- Dr. Ibe Kachikwu ya tabbatarwa 'yan Nigeria cewa har yanzu akwai isasshen man fetur da aka fi sani da 'Premium Motor Spirit (PMS)', a fadin kasar

- Kachikwu ya ce tuni kasar ta fice daga karancin man fetur, yana mai bukatar jama'a da su daina shagala da sayen man fetur tsubi da tunanin wai zai iya karewa

- Ministan ya yi nuni da cewa isashen man fetur na kwanaki 28 ya isa ya wadatar idan har aka rinka fitar da lita miliyan 50 a kowacce rana, zai wadaci kasar

Ministan cikin gida kan harkokin albarkatun man fetur, Dr. Ibe Kachikwu a ranar Lahadi ya tabbatarwa 'yan Nigeria cewa har yanzu akwai isasshen man fetur da aka fi sani da 'Premium Motor Spirit (PMS)', a fadin kasar, don haka kar hankalin kowa ya tashi.

Kachikwu a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Legas ya ce tuni kasar ta fice daga karancin man fetur, yana mai bukatar masu ababen hawa da su daina shagala da sayen man fetur din tsubi da tunanin wai zai iya karewa.

"Zan iya cewa babu wani dalili da za a samu karancin man fetur. Mun dade da fita daga wannan karnin na karancin man. Kamfanin NNPC ya tabbatar mun cewa akwai isasshen man fetur.

KARANTA WANNAN: 'Matakan da ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen matsalar man fetur'

Muna da isasshen man fetur - Kachikwu ya tabbatarwa 'yan Nigeria

Muna da isasshen man fetur - Kachikwu ya tabbatarwa 'yan Nigeria
Source: Depositphotos

"Jiya (Asabar), na ga yadda aka fara yin layi wajen shan mai a Abuja, amma an sanar da ni tangardar raba mai ce karkashin gidauniyar PEF, kuma za a magance matsalar cikin gaggawa.

"Don haka wannan ba wai matsala ba ce ta karancin mai, kamfanin ya sanar da ni akwai isasshen mai na kwanaki 28, tun a makonni biyu da suka gabata, a yanzu haka suna da man da zai kai har nan da kwanki 14 ko 15 a gaba," a cewar sa.

Ministan ya yi nuni da cewa isashen man fetur na kwanaki 28 ya isa ya wadatar idan har aka rinka fitar da lita miliyan 50 a kowacce rana, zai wadaci kasar.

Rahotanni dai sun bayyana cewa babu wani layi a kusan gidajen man fetur da ke kan hanyar filin jirgin sama na Abuja, da kuma bbar hanyar Kubwa.

Kamfanin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa masu ababen hawa na sayen man fetur cikin sauki a gidan man NNPC, Conoil da NIPCO da ke kan titin filin jirgin saman, illa dai a babban gidan mai na NNPC da ke kwaryar kasuwancin birnin, inda ke da layi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel