Ekweremadu da Melaye za su nemi kujerar shugaban marasa rinjaye

Ekweremadu da Melaye za su nemi kujerar shugaban marasa rinjaye

Mun samu labari daga Jaridar The Nation cewa jam’iyyar PDP mai adawa ta fara lissafin yadda za ta raba kananan kujerun da ta ke da su a majalisar dattawan Najeriya a majalisa ta 9 mai zuwa.

Ekweremadu da Melaye za su nemi kujerar shugaban marasa rinjaye

Wasu na so Sanata Ayo Akinyelure ya gaji Olujunmi a Majalisa
Source: UGC

Daga cikin Sanatocin jam’iyyar PDP da ake tunani za a ba mukamin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa akwai Sanata Ike Ekweremadu, wanda yake rike da mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Sauran wadanda ka iya neman wannan kujera su ne Sanata Dino Melaye na Kogi ya Yamma da kuma Ayo Akinyelure mai wakiltar yankin Ondo ta tsakiya a majalisar dattawa. Wadannan Sanatoci duk sun fito ne daga PDP.

Kamar yadda labari ya zo mana, jam’iyya ta na so Sanata Ike Ekweremadu ya samu wannan matsayi ganin irin gogewar da yake da ita a majalisa. Sai dai kuma wasu masu ruwa-da-tsaki a tafiyar PDP su na ganin ba haka ba.

KU KARANTA: Wani Sanata ya fasa kwan yadda PDP ke neman karbe Majalisa

Jaridar tace za ta so a samu irin su Sanata Ike Ekweremadu a matsayin shugaban marasa rinjaye domin jam’iyyar ta fara dakun yadda za ta karbe shugabancin majalisar daga hannun jam’iyyar APC mai mulki nan gaba kadan.

Wani Jigon PDP yana ganin Ike Ekweremadu ne ya dace ya rike kan Sanatocin adawa a majalisa domin a rika takawa APC burki a majalisar dattawan kasar. Sai dai ‘yan siyasan Arewa da kasar Yarbawa ba su gamsu da hakan ba.

KU KARANTA: Sababbin Sanatocin PDP na shirin billowa APC ta bayan gida

Wani Jagoran ‘yan siyasar PDP a kasar Yarbawa Asipa Iyanda Adeoye Ogunfojuri, a wani jawabi da ya fitar tare da Ameen Adekanye sun nemi jam’iyyar adawa ta PDP da ta rika damawa da Sanatocin Kudu maso Yammacin kasar.

Mutanen kasar Kudu ta Yamman su na so ne Sanata Ayo Akinyelure ya gaji Biodun Olujunmi wanda ta rasa tazarce a zaben bana. Olujunmi ta fito ne daga jihar Ekiti don haka Yarbawa su ke ganin su ke da wannan kujera a yanzu.

Haka kuma ‘Yan siyasar Arewa ta tsakiya su na ganin Dino Melaye na yankin ne ya fi dacewa da wannan kujera ganin yadda tsakiyar Arewa ta rasa shugaban majalisar dattawa watau Bukola Saraki a zaben 2019 a jihar sa ta Kwara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel