Atiku ya yi magana a kan zargin APC na cewa shi dan asalin kasar Kamaru ne

Atiku ya yi magana a kan zargin APC na cewa shi dan asalin kasar Kamaru ne

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce ta tabbata ya yi gaskiya a korafinsa a kan cewar zaben shugaban kasar Najeriya da aka yi, cike ya ke da magudi kuma sakamakon da aka bayyana ba shine abinda jama'a suka zaba ba.

Ya ce amsar dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Shugaba Buhari, da kuma wacce jam'iyyarsa, APC, suka bayar a kan karar da ya shigar, su ne hujjar sa.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun kakakinsa, Mazi Paul Ibe, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya yanke shawarar kalubalantar APC da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a kotu, saboda yana da kwararan hujjoji. Kazalika ya kalubalanci APC da INEC da zu fito da hujjojin da zasu rushe na sa, ba a fake da wasu maganganu na soki burutsa a kan asalin kasar da ya fito ba.

"Jam'iyyar APC ta zabi kare kanta ta hanyar bullo da wasu maganganu masu ban dariya a kan cewar Wazirin Adamawa ba dan Najeriya ba ne, hakan ya nuna mana irin mutanen da ke APC da gwamnatinta, wacce wa'adinta na halak zai kare a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.

Atiku ya yi magana a kan zargin APC na cewa shi dan asalin kasar Kamaru ne

Atiku Abubakar
Source: Twitter

"Matakin da APC ta dauka a kan karar da Atiku ya shigar da ita, ya nuna maitar su na son makale wa a karagar mulki ta kowanne hali, a saboda haka tsohon mataimakin shugaban kasa ba zai mayar da wani martani a kan wannan zance mai kama da wasan yara ba. Lauyoyinmu zasu yi abinda ya dace a kotu.

DUBA WANNAN: An kama 'yan sanda 5 a Legas bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 20 da wani mutum

"Abinda nake so 'yan Najeriya su gane a nan shine, jam'iyyar APC ta bullo da wannan magana ne bayan ta fahimci cewar ta canja zabin 'yan Najeriya sannan ba ta da hujjar kare kanta. Jama'a su sani cewar kundin tsarin mulki ya riga tutuni ya fadi waye dan Najeriya, a saboda haka jam'iyyar APC ba ta da ikon fadin waye dan Najeriya ko ba dan Najeriya ba," a cewar jawabin.

Sanarwar ta yiwa 'yan Najeriya tuni cewar Atiku ya yi aiki ga kasa tukuru a matakai daban-daban daga aikin gwamnati zuwa siyasa, har ga zuwa matakin mataimakin shugaban kasa da ya rike na tsawon shekaru 8.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel