'Matakan da ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen matsalar man fetur'

'Matakan da ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen matsalar man fetur'

- Farfesa Cecilia Olufunke-Akintayo, ta shawarci gwamnati tarayya da ta gina sabbin kamfanonin sarrafa sinadaran 'Chemicals' na zamani

- A cewar ta idan har aka samar da kamfanonin, hakan zai kawo karshen matsalar man fetur da 'yan Nigeria ke fama ita da kuma ragewa gwamnatin nauyin rarraba man

- Olufunke-Akintayo ta ce, hakan zai samar da hanyar rage amfani da kayayyakin da aka sarrafa daga fetur da kuma wasu sinadaran da ke da illa ga rayuwa da muhalli

Farfesa Cecilia Olufunke-Akintayo, ta shawarci gwamnati tarayya da ta gina sabbin kamfanonin sarrafa sinadaran 'Chemicals' na zamani, da za su iya samar da man fetur daga sinadaran, a mai makon mayar da hankali kan man fetur da aka fi sani da 'Premium Motor Spirit, (PMS)'.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa Olufunke-Akintayo, wacce farfesa ce a ilimin Chemistry a masana'ance daga jami'ar gwamnatin tarayya da ke Oye, jihar Ekiti, ta bayar da wannan shawarar a yayin da ta ke gabatar da wata lakca a jami'ar a ranar Lahadi.

Ta ce idan har gwamnati ta samar da kamfanonin to hakan zai kawo karshen matsalar man fetur da 'yan Nigeria ke fama ita da kuma ragewa gwamnatin nauyin rarraba man fetur din.

KARANTA WANNAN: Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta cafke wadanda suka yi garkuwa da wani dan jarida

'Matakan da ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen matsalar man fetur'

'Matakan da ya kamata gwamnatin tarayya ta dauka domin kawo karshen matsalar man fetur'
Source: Facebook

A cewar ta, hakan zai samar da hanyar rage amfani da kayayyakin da aka sarrafa daga fetur da kuma wasu sinadaran 'chemicals' da ke da illa ga rayuwa da muhalli.

Wannan kiran na ta ya zo ne jim kadan bayan da shugaban jami'ar, Farfesa Kayode Shoremekun, ya bayyana cewa akwai karancin masana'antun sarrafa man fetur daga sinadaran 'chemicals' da kuma tama-da-karafa a kasar.

Har ila yau Olufunke-Akintayo ce ke shugabantar kwamitin tsare tsaren ilimi na jami'ar.

Farfesar ta ce akwai bukatar gaggawa na Nigeria ta yi watsi da kayayyakin da aka sarrafa su daga sinadaran fetur da 'chemicals' saboda illarsu ga dan Adam da kuma muhalli, ma damar ana so a alkinta muhalli da dorewar rayuwar jama'a.

Ta bayyana cewa amfani da kayayyakin da aka sarrafa da ga sinadaran da Allah ya samar zai tabbatar da dorewar tattalin arziki, ababen more rayuwa da kuma dorewar muhalli a kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel