Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta cafke wadanda suka yi garkuwa da wani dan jarida

Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta cafke wadanda suka yi garkuwa da wani dan jarida

- Rundunar 'yan sanda ta ce ta cafke wadanda da ake zargin sun yin garkuwa da wani ma'aikacin gidan talabijin na Channels TV, Mr Friday Okeregbe

- Okeregbe wanda ya kubuta a ranar 28 ga watan Maris, wasu 'yan bindiga da ba asan ko su waye ba sun sace shi ne a ranar 22 ga watan Maris a Abuja

- Wadanda ake zargin sun hada da: Hanniel Patrick, 29, daga Akwa Ibom, Abdulwahab Isah, 28 da Salisu Mohammed, 32 dukkaninsu daga Kogi

Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar cafke mutane ukku da ake zarginsu da sa hannu a yin garkuwa da wani wakilin gidan talabijin na Channels TV, Mr Friday Okeregbe.

Wadanda ake zargin sun hada da: Hanniel Patrick, 29, daga Akwa Ibom, Abdulwahab Isah, 28 da Salisu Mohammed, 32 dukkaninsu daga Kogi.

Okeregbe wanda ya kubuta a ranar 28 ga watan Maris, wasu 'yan bindiga da ba asan ko su waye ba sun sace shi ne a ranar 22 ga watan Maris akan hanyar 'Games Village' a Abuja a yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa wajen bakanikensa.

KARANTA WANNAN: NLC: Mun ba Buhari nan da 1 ga Mayu ya rattaba hannu kan dokar karin albashi

Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta cafke wadanda suka yi garkuwa da wani dan jarida

Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta cafke wadanda suka yi garkuwa da wani dan jarida
Source: UGC

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, Mr Frank Mba, kuma mataimakin kwamishina, a ranar Lahadi a Abuja, ya ce rundunar atisayen 'Puff Adder' sune suka cafke wadanda ake zargin a ranar 9 ga watan Afrelu.

Ya ce Okeregbe wanda ba shi ne wanda suka so yin garkuwa da shi ba, sun kai shi mabuyar 'yan ta'addar da ke arimo, Abuja, inda suka boye shi ba tare da sanin inda ya ke ba.

Mai magana da yawun rundunar ya ce an kwato wasu kayayaki daga hannun wadanda aka cafken da suka hada da bindiga kirar cikin gida, sai alburusan bindiga kirar AK47, gatarin fada, wayoyin hannu da kuma fuskokin badda kama da suke rufe idanuwa wadanda suka fada komarsu.

Mba ya ce wadanda aka cafken sun baiwa rundunar muhimman bayanai.

Ya ce yanzu haka rundunar na iya bakin kokarinta na gain ta cafke sauran mambobin tawagar da suke da yawa.

Mba ya ce Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mr Mohammed Adamu ya baiwa 'yan Nigeria tabbacin cewa rundunar da sauran jami'an tsaro za su yi duk mai yiyuwa na ganin sun kawo karshen ta'addin a kasar.

Sai dai, ya bukaci daukacin jama'a da suka kasance ma su baiwa rundunar 'yan sanda kwararan bayanai da su taimaka wajen cafke dukkanin masu aikata laifukan ta'addanci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel