Gobara ta kone shaguna 6 a babbar kasuwar jihar Kebbi

Gobara ta kone shaguna 6 a babbar kasuwar jihar Kebbi

Da sanadin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wutar gobara ta yi mugunyar ta'adi a babbar kasuwar jihar Kebbi, inda kimanin shaguna 6 suka kone kurmus tare da dukkanin wata tarin dukiya da ke cikin su.

A ranar Juma'ar da ta gabata wuta ta kone kimanin runfuna shida da ke babbar kasuwar jihar Kebbi yayin da tsautsayi na gobara ya auku cikin duhun dare.

Gobara ta kone shaguna 6 a babbar kasuwar jihar Kebbi

Gobara ta kone shaguna 6 a babbar kasuwar jihar Kebbi
Source: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, wutar ta lakume shaguna shida daura da yankin masu sayar ga magunguna da kayayyaki na harkokin noma a gabar babbar kasuwar garin Birnin Kebbi.

Daya daga cikin masu aikin gadi a kasuwar, Mallam Aminu Shehu yayin ganawar sa da manema labarai ya bayyana cewa, kawowa yanzu ba bu masaniya ta dalilin da ya haddasa aukuwar gobarar.

Shehu ya ce taimakon jami'an hukumar kwana-kwana ya sanya a ka samu nasara wajen dakile ci gaba da aukuwar barna ta gobarar da misalin karfe 10.00 na yammaci.

KARANTA KUMA: Lauyan Atiku ba ya da lasisin shiga harkokin shari'a a Najeriya - INEC

Kazalika daya daga cikin mamallakan shagunan kuma wakilin saye da sayarwa da kamfanin Saro Agro mai harkokin magunguna da kayayyakin noma, Mallam Muhammad Lawal, ya ce gobarar ta haifar masa da asarar ta dukiya mai tarin yawa ta kimanin Miliyoyin Naira.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel