NLC: Mun ba Buhari nan da 1 ga Mayu ya rattaba hannu kan dokar karin albashi

NLC: Mun ba Buhari nan da 1 ga Mayu ya rattaba hannu kan dokar karin albashi

- NLC ta baiwaBuhari wa'adin nan da 1 ga watan Mayu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta kara mafi karancin albashi zuwa N30,000

- Kwamred Ayuba Wabba, shugaban NLC na kasa, ya bayar da wannan wa'adin a ranar Asabar a wata zantawarsa da manema labarai a Abuja

- Ayuba Wabba ya ce har yanzu babu wanda ke da amsa kan cewa tun a baya akwai tallafin man fetur ko babu, kasancewar an lalata darajar kudaden

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa'adin nan da 1 ga watan Mayu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta kara mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar daga N18,000 zuwa N30,000.

Kwamred Ayuba Wabba, shugaban NLC na kasa, ya bayar da wannan wa'adin a ranar Asabar a wata zantawarsa da manema labarai a Abuja.

"Tunanin kowanne ma'aikaci ba zai wuce ya ga shugaban kasa ya rattaba hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashin ba, kuma muna son nan da 1 ga watan Mayu ya yi hakan. Wannan shi ne matsayar da muka cimmawa kuma muna fatan shugaban kasar zai aikata hakan kafin wa'adin," a cewar Wabba.

KARANTA WANNAN: Shekaru 5: Yadda gwamnatin Buhari ta gaza ceto 'yan matan Chibok - BBOG

NLC ta baiwa Buhari nan da 1 ga watan Mayu ya rattaba hannu kan dokar karin albashi

NLC ta baiwa Buhari nan da 1 ga watan Mayu ya rattaba hannu kan dokar karin albashi
Source: Twitter

"Muna son ya zamana cewa akwai wa'adi ta yadda ma'aikata za su fara samun sabon mafi karancin albashin a aljihunansu, matsalar tattalin arziki na ci gaba da kuntatawa jama'a musamman wadanda karin albashin bai kai ga shafarsu ba."

Ya kuma yi tsokaci kan wani ikirari da gwamnatin tarayyar ta yi na cewar za ta kara farashin man fetur, yana mai cewa: "Tun a tashin farko, da ma akwai tallafin manftur ne? Wannan tambaya ce da har yanzu babu wanda ya amsa.

"Kamar yadda shugaban kasar ya ambata, tallafin mai cin hanci ne kuma muna yaki da hakan. Za mu rinka yin batun tallafin man fetur idan har ba mu samar da danyen mai. Har yanzu sun gaza gyara matsalar kudadenmu. Muna biyan ayyukan da ba su gamshi kowa ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel