Lauyan Atiku ba ya da lasisin shiga harkokin shari'a a Najeriya - INEC

Lauyan Atiku ba ya da lasisin shiga harkokin shari'a a Najeriya - INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta ce korafin da Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya shigar ba ya da nasaba da sa hannun wani lauya mai lasisin shiga harkokin shari'a a Najeriya.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, hukumar INEC ta ce korafin da Atiku ya gabatar a gaban kotun bai samu sa hannu na Lauya mai lasisin shiga harkoki na shari'a a Najeriya ba.

Ko shakka ba bu Atiku wanda ya kasance tsohon shugaban kasar Najeriya ya shigar da korafi a gaban kotun daukaka kara domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Lauyan Atiku ba ya da lasisin shiga harkokin shari'a Najeriya - INEC

Lauyan Atiku ba ya da lasisin shiga harkokin shari'a Najeriya - INEC
Source: Twitter

Atiku yayin hawa kujerar naki ta amincewa da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, na ci gaba da neman hakkin sa a shari'ance in da lauyoyi kimanin 32 ke wakiltar sa bisa jagorancin wani zakakurin Lauya, Livy Uzoukwu.

Sai dai cikin mayar da martanin tuhumar da ke kanta, hukumar INEC ta ce Lauyan Atiku baya da cancantar shiga al'amura na shari'a a Najeriya sakamakon rashin samun lasisi wakilci na shari'a daga kotun koli ta kasar nan.

KARANTA KUMA: Yawan shigowar baki ya sanya cutar Kanjamau ta zama ruwan dare a jihar Akwa Ibom

Yayin ganawar ta da manema labarai a watan Maris da ya gabata, tawagar lauyoyi masu kare Atiku ta yi furuci na samun wadatattun hujjoji gami da dalilai na kalubalantar sakamakon zaben kujerar shugaban kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel