Ban manta da labarin ‘Yan Matan Chibok ba – Inji Shugaba Buhari

Ban manta da labarin ‘Yan Matan Chibok ba – Inji Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa Iyayen yaran da aka sace a Makarantar sakandaren nan da ke Garin Chibok cewa bai manta da ‘Ya ‘yan su da aka yi gaba da su tun a shekarar 2014 ba.

Shugaba Buhari yayi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun bakin sa watau Malam Garba Shehu. Shugaban kasar ya sake jaddada alkawarin sa da yayi na cewa zai kubuto da duk Yaran da su ke hannun Boko Haram.

Garba Shehu a wannan jawabi da ya fitar a Ranar da aka cika shekaru 5 da sace ‘Yan makarantar na Chibok yace shugaban kasar bai manta da ragowar wadannan Yara da ke tsare a hannun ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram ba.

KU KARANTA: Wani babban 'Dan siyasa yayi lalata da Matar Makwabcinsa

Ban manta da labarin ‘Yan Matan Chibok ba – Inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yace wadanda aka sace a Chibok za su fito
Source: UGC

Jawabin yana cewa:

Buhari yana sane da alkawarin da yayi, wannan ne ma babban dalilin da ya sa mutanen Chibok su ka fito su ka mara masa baya a zaben da aka yi kwanakin baya, kuma duk da an ceto yara 107, Buhari ba zai zauna ba har sai an gano dukkansu.

Haka zalika shugaban kasar ya kuma yi magana a kan Leah Sharibu wanda aka sace a wata makarantar gwamnati da ke cikin Garin Dapchi a jihar Yobe kwanaki, inda yace ita ma tana daf da komawa gaban Iyayen ta, ba da dadewa ba.

Shugaban kasar ya aika da gaisuwar musamman ga sauran ‘Yan matan Chibok fiye da 100 da gwamnatin tarayya ta ke daukar nauyin karatun sa a babbar jami’ar nan ta Amurka da ke Garin Yola da sauran makarantun Duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel