Shekaru 5: Yadda gwamnatin Buhari ta gaza ceto 'yan matan Chibok - BBOG

Shekaru 5: Yadda gwamnatin Buhari ta gaza ceto 'yan matan Chibok - BBOG

- Oby Ezekwesili, ta kalubalanci gwamnatin Buhari na gaza kwato sauran 'yan matan da suka rage a hannun Boko Haram tsawon shekaru biyar

- Ta yi mamakin dalilin da zai sa gwamnati ta yi gum da bakinta akan sako 'yan matan, tana mai cewa har yanzu babu wasu bayanai daga Buhari kan sako 'yan matan

- A hannu daya kuwa, shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa har yanzu bai manta da yan matan Chibok ba, kuma zai kubutar da su

Wacce ta assasa kungiyar da ke fafutukar ganin an kwato 'yan matan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram suka sace (BBOGC), Oby Ezekwesili, ta kalubalanci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari na gaza kwato sauran 'yan matan da suka rage a hannun Boko Haram tsawon shekaru biyar da sace su.

A ranar 14 ga watan Afrelu, 2014, akalla 'yan matan makarantar sakandire ta Chibok da ke jihar Borno guda 276 ne mayakan Boko Haram suka sace su. Daga baya dai kalilan ne aka samu nasarar kubuto da su.

Tsohowar ministar ilimin, a shafinta na Twitter, a ranar Asabar, ta bayyana cewa shirun da gwamnatin tarayya ta yi na sako sauran 'yan matan da har yanzu ke hannun Boko Haram abun kunya ne, tana mai cewa abun takaici ne a ce har yanzu an gaza kubuto da 'yan matan bayan shekaru biyar.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: An dakatar da Osita Chidoka, mai magana da yawun Atiku Abubakar

Shekaru 5 da sace 'yan matan Chibok: Gwamnatin tarayya ta gaza - BBOG

Shekaru 5 da sace 'yan matan Chibok: Gwamnatin tarayya ta gaza - BBOG
Source: UGC

Ta yi mamakin ko shugaban kasar zai cika alkawarin da ya dauka na ceto 'yan matan gaba daya, tana mai cewa abun kunya ne ga gwamnatin shugaban kasa Buhari a ce har yanzu babu amo ba labari kan ceto 'yan matan.

Ta yi mamakin dalili da zai sa gwamnati ta yi gum da bakinta akan sako 'yan matana, tana mai cewa "Har yanzu babu wasu bayanai daga gwamnatin Buhari kan sako 'yan matan. Abun kunya ne wannan. Babban abun kunya. Ba zamu taba mantawa da su ba. Me kuma ya rage mu fada?"

Ta yi nuni da cewa lakcar shekara shekara da aka saba gabatarwa kan 'yan Matan Chibok din, a bana ta canja salo, taken lakcar 2019 shi ne: Bakin cikin sace 'yan matan Chibok: A gobe (Alhamis) ne za a gabatar da makala kan kunyatacciyar kasa, yayin da Aisha Abubakar za ta zama babbar mai gabatar da jawabi, yayin da Aiyyah Yesufu za ta gabatar da jawabin sako na musamman domin tunawa da ranar.

A hannu daya kuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar asabar ya baiwa iyayen 'yan matan makarantar Chibok da har yanzu ke hannun Boko Haram tabbacin cewa har yanzu bai manta da yaran ba, wadanda aka sace su tun shekaru biyar da suka gabata.

A cikin wata sanarwa daga Garba Shehu, babban mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar watsa labarai a Abuja ya yi tuni da cewa shugaba Buhari ya sha alwashin kubuto da sauran 'yan matan a farkon wa'adin mulkinsa, kuma zai cika wannan alkawarin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel