Yawan shigowar baki ya sanya cutar Kanjamau ta zama ruwan dare a jihar Akwa Ibom

Yawan shigowar baki ya sanya cutar Kanjamau ta zama ruwan dare a jihar Akwa Ibom

A sanadiyar sakamakon binciken da aka gudanar kan yaduwar cutar kanjamau a Najeriya, gwamnatin jihar Akwa Ibom ta alakanta yadda cutar kanjamau ta zama ruwan dare a fadin jihar da yawan shigowar baki.

Binciken da hukumar kula da yaduwar cutar kanjamau a Najeriya ta gudanar a kwana-kwanan nan ya tabbatar da cewa, jihar Akwa Ibom ta yiwa sauran jihohin Najeriya zarra da fintinkau ta fuskar yawan adadi na masu dauke da kwayoyin cutar mai karya garkuwar jiki.

Gwamnan jihar Akwa Ibom; Udom Gabriel Emmanuel

Gwamnan jihar Akwa Ibom; Udom Gabriel Emmanuel
Source: Depositphotos

Kimanin kaso 5.5 cikin 100 na adadin al'ummar Najeriya masu dauke da kwayoyi na cutar kanjamau sun kasance a jihar Akwa Ibom, inda jihar Benuwai ke take ma ta baya da kaso 5.3 kamar yadda sakamakon binciken da aka wassafa a ranar 14 ga watan Maris ya bayyana.

A yayin da jihar Akwa Ibom ta kasance a mafi kololuwar mataki na yawan adadin al'umma masu dauke da kwayoyi na cutar kanjamau, kwamishinan lafiya na jihar, Dominic Ukpong yayin ganawar sa da manema labarai ya yi sharhi akan wannan mummunan kalubale.

Mista Ukpong yayin bayar da tabbacin sa akan yadda ake samun rangwami na yawan adadin masu dauke da cutar kanjamau a jihar Akwa Ibom, ya ce yawaitar yaduwar cutar na da alaka mai girman gaske da yadda ake samun shigowar baki daga dukkanin lunguna da sako da ta kunsa.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Rayukan Yara 432 sun salwanta a Arewa maso Gabas cikin shekarar 2018 - UNICEF

Kazalika kwamishinan na lafiya ya bayar da tabbacin sa a kan yadda gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumomi, kungiyoyi da kuma cibiyoyin lafiya na duniya wajen daura damara tare da shimfida matakan tsaro na dakile yaduwar cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel