Ba za mu bari a maimata abin da Saraki yayi a baya, a zaben bana ba – Sanatan APC

Ba za mu bari a maimata abin da Saraki yayi a baya, a zaben bana ba – Sanatan APC

Wasu Sanatocin jam’iyyar APC su na zargin cewa jam’iyyar adawa ta PDP tana da nufin karbe majalisar tarayya a wannan karo. Jam’iyyar hamayyar za tayi haka ne ta hanyar yin zaben bana a boye.

Wani sabon Sanatan APC da ba a bayyana sunan sa ba, ya bayyana cewa ‘Yan majalisan PDP su na shirya yadda majalisa za ta sake dawowa hannun su wannan karo. Sanatan yace za ayi kokarin yin zaben ‘yan majalisun ne a asirce.

Wannan Sanata da ya ki bayyana kan sa, ya bayyanawa majiyar mu cewa PDP za tayi amfani da Akawun majalisa wanda zai bada damar ayi aiki da dokar da aka yi aiki da ita a zaben 2015 wanda har ya kai Bukola Saraki ya zama shugaba.

KU KARANTA: Kotu ta nemi su Saraki su kare kan su a gaban shari’a

Ba za mu bari a maimata abin da Saraki yayi a baya, a zaben bana ba – Sanatan APC

PDP na da shirin karbe Majalisa daga hannun APC a 2019
Source: Facebook

Dokokin majalisar da aka yi amfani da su a 2015, sun bada dama ne ‘yan majalisun tarayyar su zabi shugabanni a boye ba tare da Duniya ta san kuri’ar da kowane Sanata ya kada ba. Wannan Sanata na APC ya nuna hakan bai dace ba.

Sabon-shiga majalisar ya sha alwashi cewa ba za su bari ayi zaben shugabannin bana a boye ba, inda yace kusan ko ina a Duniya, a kan yi zaben wadanda za su jagoranci ragamar majalisa ne a bayyane, ba tare da wani boye-boye ba.

‘Dan majalisar ya kara da cewa a 2015, APC ta raina PDP inda yace ba su taba tunanin cewa abin da ya faru a majalisar zai farun ba, don haka yace a wannan karo, APC ba za ta sake yin irin wancan shirmen da tayi har ta rasa majalisar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel