DCP Abba Kyari ya cafke wasu manyan masu satar mutane a Imo

DCP Abba Kyari ya cafke wasu manyan masu satar mutane a Imo

Mun samu labari daga Daily Trust cewa wasu masu garkuwa da mutane har mutum 7 da aka kama kwanan nan sun bayyana yadda su kashe wani Ba’Amurke a cikin jihar Imo a shekarar 2017 da ta wuce.

Wadannan manyan masu laifi sun shiga hannun babban jami’in Dan Sanda DCP Abba Kyari da ‘Yan Tawagarsa na IRT ta musamman. Sunayen wadanda aka kama ake zargi da aikata wannan laifi ya shiga hannun ‘ya jarida.

Jami’an tsaron sun ce wadanda su ka damke su ne; Sunday Igwe, Michael Ahmefula, Oyebuchi Echefule, Ndubusi Isaac, Victor Dagogo, Chima Okoro da kuma John Edet. Sunday Igwe shi ne wanda aka fi sani da suna Star Boy.

A jawabin da wadannan mutane da ake zargi da laifin satar jama’a da kisa da garkuwa da mutane su ka bada, sun tabbatar da cewa su ne ke yin fashi da makami, sannan kuma su kan tsare mutane a yankin Imo, Abia da Ribas.

KU KARANTA: Amurka ta gargadi mutanen ta a kan zuwa Najeriya saboda rashin tsaro

DCP Abba Kyari ya cafke wasu manyan masu satar mutane a Imo

Barayin su ka fitini Jihohin Kudancin Najeriya sun shiga hannun ‘Yan Sanda
Source: Twitter

Jagoran wannan Tawaga watau School Boy, ‘dan asalin jihar Abia, mai shekaru 29 a Duniya ya bayyana yadda su ka kashe wannan sojan kasar Amurka da su ka taba kamawa. Igwe dai yayi watsi ne da karatun Boko tun a Sakandare.

Gawurtaccen ‘dan fashin da aka fi sani da School Boy yake cewa sun kashe wannan Ba Amurke ne bayan sun gano cewa yana dauke da bindiga a jikinsa, inda yace da ba su kashe sa ba, da tuni ya hallaka su lahira babu wata-wata.

Sunday Igwe yace wannan Sojan kasar waje ya shiga harbin su ne da bindigarsa inda a karshe ya harbi Direban motarsu da kuma shi kan sa Jagoran na su wanda hakan ta sa dole su ka harbe sa, kuma su ka jefar da gawar a cikin kwata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel