Stella Emelife Chinello ta lashe kyaututtuka fiye da 20 a Jami’ar Mysore

Stella Emelife Chinello ta lashe kyaututtuka fiye da 20 a Jami’ar Mysore

Wata Hazikar ‘daliba da ta kammala jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke jihar Sokoto kwanakin baya ta sake nuna bajintar ta, bayan da ta karya tarihin da aka bari a jami’ar kasar wajen da ta je karo karatu.

Stella Emelife Chinello, wanda ta gama jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto da ajin farko na Digiri (watau First class) a fannin kimiyya na Chemistry, ta kafa tarihi a jami’ar Mysore da ke kasar Indiya kwanakin baya.

Shugaban jami’ar UDUS, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru yace wannan Baiwar Allah ta lashe kyaututtuka na gwal har 20 da kuma lambar yabo iri-iri na kudi a lokacin da aka yi bikin yaye ‘daliban makarantar na karo na 99.

KU KARANTA: Dattawa sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari a kan matsalar tsaro

Stella Emelife Chinello ta lashe kyaututtuka fiye da 20 a Jami’ar Mysore

Stella Chinello ta kafa sabon tarihi a Jami'ar Mysore
Source: UGC

Farfesa Abdullahi Zuru yayi wannan jawabi ne a Ranar Juma’a 12 ga Watan Afrilun 2019 wajen taron bikin yaye ‘daliban jami’ar jami’ar ta UDUS da aka yi. Jami’ar ta yaye dalibai fiye da 12, 000 a wannan karo inji Farfesan.

Daga cikin ‘daliban da aka yaye, an samu fiye da 100 daga ciki da su ka kammala karatu da ajin farko na matakin Digiri na First Class. Stella Chinello da kuma wata Zainab Abdullahi Bashir su na cikin wadanda su kayi fice.

Abdullahi Zainab wanda ta fito daga jihar Katsina ta gama karatu ne a bangaren Physics da maki 4.81 cikin 5.0. A tarihin jami’ar tarayyar ta Sokoto, Zainab ce macen farko da aka fara yayewa da wannan mataki a wannan fanni.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel