Alkali Abang yana so ‘Yan Majalisar da su ka sauya-sheka su kare kan su

Alkali Abang yana so ‘Yan Majalisar da su ka sauya-sheka su kare kan su

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Garin Abuja,ta ba Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara wadanda su ne shugabannin majalisar wakilan kasar nan, lokaci da suyi maza su bayyana a gaban ta.

Mun ji cewa Alkali mai shari’ar Okon Abang na kotun babban birnin tarayya ya nemi Sanatocin kasar nan 18 da kuma ‘Yan majalisun wakilai na tarayya 36, har da Ministan shari’an Najeriya, su shirya zuwa gaban kotun sa.

Har wa yau bayan Bukola Saraki da Takwaransa Yakubu Dogara, sauran wadanda Alkali Okong Abang yake so su hallara a gaban sa akwai mataimakan shugabannin majalisar kasar watau Ike Ekweremadu da Yusuf Lasun.

Kotu tana so wadannan manyan ‘Yan majalisa su kare kan su ne game da karar su da ake yi a kan canza sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wancan a kwanakin baya. Haka zalika INEC za ta bayyana wajen wannan shari’a.

KU KARANTA: Kwamitin Goje sun gaza gabatar da aikin kasafin kudi a gaban Majalisa

Alkali Abang yana so ‘Yan Majalisar da su ka sauya-sheka su kare kan su

Ana karar Bukola Saraki da wasu 'Yan Majalisa a kan sauya-sheka
Source: Depositphotos

Babban Alkalin da ke wannan shari’a a Abuja ya yanke hukuncin cewa dole wadanda ake tuhuma su zo gaban kotu su wanke kan su. Alkalin ya kuma ki bada wani sassauci inda yace dole wadanda ake karar su tako kafa wurin sa.

Alkali ya bada nan zuwa 18 ga Watan Afrilu domin wadanda ake tuhuma da laifi su gabatarwa kotu da hujjojinsu. An shirya karashe wannan shari’a dai tun a makon jiya inda ‘yan majalisun da ake kara su ka halarci zaman kotun.

Manyan ‘yan majalisar dattawan da ake tuhuma da laifin sauya-sheka sun hada da irin su Bukola Saraki, Rabiu Musa Kwankwaso, Shaaba Lafiagi, da kuma Godswill Akpabio wanda ya bar PDP zuwa APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel