Shugaba Buhari ya halarci taron CED-SAD a N'Djamena (Hotuna)

Shugaba Buhari ya halarci taron CED-SAD a N'Djamena (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron taron shugabani kasashen nahiyar Afrika da ke yankin Sahel Sahara, CEN-SAD inda ya gabatar da jawabi kan abubuwan da suka shafi tsaron Najeriya.

Buhari da sauran shugabannin kasashen yankin sun hadu ne da mai masaukin bakinsu kuma shugaban CEN-SAD, Shugaba Idriss Deby Itno domin tattaunawa a kan harkokin siyasa da tsaro da sauransu.

Daga cikin shugabannin kasan da suka halarci taron sune shugaban kasar Nijar, Mohammad Issoufou; da shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe.

Hotunan taron CED-SAD da Buhari ya halarta a N'Djamena

Hotunan taron CED-SAD
Source: Facebook

Shugaba Buhari ya yi magana da babban murya kan yadda makamai ke shigowa Najeriya kuma yake fadawa hannun ya bindiga da suka fara zama kalubale ga zaman lafiyar yan Najeriya.

Saboda haka ya yi kira da hadin kai tsakanin kasashen Sahel da Sahara kan yadda za'a shawo kan al'amarin.

Cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa , Mallam Garba Shehu,yayi, ya ce kasar Najeriya ta kasance tana aiki da makwabtanta wajen hana shigowa da wadannan makamai, “amma sai dai habbakar da abin ke kara yi a yanzu yana kara samun cigaba” ya zama dole a garemu mu sake fadada neman goyon bayan sauran kasashen domin ganin an shawo kan matsalar.

Hotunan taron CED-SAD da Buhari ya halarta a N'Djamena

Hotunan taron CED-SAD da Buhari ya halarta a N'Djamena
Source: Facebook

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin N'Djamena babban birnin kasar Chadi a ranar Asabar 13 ga watan Afrilun 2019 domin hallartan taronn.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ta ruwaito cewa jirgin shugaban kasar da tawagarsa ciki har da wasu gwamnoni uku sun sauka a filin tashi da saukan jirage na Hassan Djamous International Airport N’Djamena misalin karfe 9.40 na safe.

Hotunan taron CED-SAD da Buhari ya halarta a N'Djamena

Hotunan taron CED-SAD da Buhari ya halarta a N'Djamena
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel