Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo Najeriya

Yanzu-yanzu: Buhari ya dawo Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja daga N'Djamena, kasar Chadi, inda ya halarci taron gangamin shugabannin kasa da gwamnatocin kasashen Sahel (CEN-SAD) ranar Asabar, 13 ga wtaan Afrilu, 2019.

Wadanda suka raka shugaba Buhari babban filin jirgin saman Djamous domin yi masa bankwana sune jami'an gwamnatin kasar Chadi, ministan harkkin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; ministan harkokin cikin Najeriya, Abdulrahman Dambazzau da ministan tsaro, Mansur Dan-Ali.

Sauran sune, mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Mohammed Munguno; shugaban hukumar leken asirin Najeriya NIA, Ahmed Rufai Abubakar; shugaban hukumar shiga da ficen Najeriya, Mohammed Babandede; Hajiya Sadiya Umar Farouq da jakadin Najeriya a Chadi, Nasiru Waje.

A kasar Chadi, shugaba Buhari ya yi magana da babban murya kan yadda makamai ke shigowa Najeriya kuma yake fadawa hannun ya bindiga da suka fara zama kalubale ga zaman lafiyar yan Najeriya.

Saboda haka ya yi kira da hadin kai tsakanin kasashen Sahel da Sahara kan yadda za'a shawo kan al'amarin.

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin N'Djamena babban birnin kasar Chadi a ranar Asabar 13 ga watan Afrilun 2019 domin hallartan taron. Daga cikin wadanda suka taka masa baya sune gwamnonin jihar Osun, Gboyega Oyetola; na jihar Borno, Kashim Shettima, da na jihar Legas, Akinwumi Ambode.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel