An bawa hammata iska tsakanin Abdullahi Abbas da Kwankwaso

An bawa hammata iska tsakanin Abdullahi Abbas da Kwankwaso

A wani faifain bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta da Legit.ng ta ci karo da shi, an ga shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, da kwamishina raya karkara da birane, Musa Iliyasu Kwankwaso, su na bawa hammata iska.

A cikin takaitaccen faifan bidiyon, an ga shugabannin biyu na kai wa juna naushi a cikin wani daki da ya yi kama da wurin taron siyasa.

An bawa hammata iska tsakanin Abdullahi Abbas da Kwankwaso

Abdullahi Abbas da Musa Iliyasu Kwankwaso
Source: Twitter

Wasu daga cikin masu fadar albarkacin bakinsu a kan bidiyon, sun bayyana cewar a cikin gidan gwamnatin Kano ne abin ya faru.

Babu wani sautin murya da ke nuna abinda ya haddasa manyan mutanen biyu yin fada har da doke-doke a tsakaninsu.

Kalli faifan bidiyon a nan:

Koma dai mene ya faru a tsakaninsu, jama'a na ganin bai kamata a matsayinsu na jagororin jama'a da ke rike da manyan mukamai su yi wannan abin kunya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel