Buhari ya nemi goyon bayan kasashen dake makwabtaka da Najeriya wajen kare yaduwar makamai

Buhari ya nemi goyon bayan kasashen dake makwabtaka da Najeriya wajen kare yaduwar makamai

-Shigowar makaman na kawo tabarbarewar zaman lafiya a kasa tare da hasarar rayuka

-Akwai bukatar Kasashen dake cikin CEN-SAD da su kara jajircewa domin magance wannan matsalar ta tsaro

Shugaba Buhari ya nemi goyon bayan kasashen dake Sahara da Sahel dasu baiwa Najeriya gudumuwarsu wajen shawo kan matsalar yaduwar kananan makamai.

Shugaba Buhari ya lura da muhimmancin yin hakan domin yaduwar kananan makaman shi ke ba kungiyoyin ta’addanci damar mallakarsu, hakan kuwa ba karamar barazana bace ga fannin tsaro na kasa da kuma walwalar jama’a.

Ya yi jawabi a babban birnin Chadi wato N’Djamena, yayinda yaje taron kwana daya na ‘CEN-SAD’ kungiyar Shugabannin kashen yankin Sahara da kuma Sahel inda yake tare da shugaban kungiyar kuma shugaban kasar ta Chadi, Idis Deby Itno da kuma takwarorinsu na kasar Nijar da Togo.

Shugaba Buhari

Shugaba Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA:An tura wasu mutum biyu gidan kaso saboda dukan wata mata da su kayi

Cikin jawabin da mai taimakama shugaban kasa akan kafofin sadarwa da kuma yada labarai yayi, Mallam Garba Shehu a Abuja yace, kasar Najeriya ta kasance tana aiki da makwabtanta wajen hana shigowa da wadannan makamai, “amma sai dai habbakar da abin ke kara yi a yanzu yana kara samun cigaba” ya zama dole a garemu mu sake fadada neman goyon bayan sauran kasashen domin ganin an shawo kan matsalar.

Haka zalika, Shugaban kasa yace ficewa daga kasar Najeriya zuwa wasu kasashe ba abisa ka’ida ba musamman tsakanin mata da kananan yara ya kasance babban barazana ga lamuran tsaro a kasar nan.

A cewar tasa “Duba da irin ayyukan da suka wajaba akan wannan kungiya akan harkokin tsaron cikin gida, Shugaba Buhari ya nemi kasashen da ke ciki da su kara hada kai domin ganin cewa sun kawar da matsalolin dake ci masu tuwo a kwarya.

“Yayinda yake birnin N’Djamena, Shugaba ya yi magana akan yan Najeriya da suke zaune a kasar Libya inda wa sunsu ake muzguna masu, da a barsu su wala, wannan ma yana daga cikin aikin CEN-SAD wacce take da sakatariyarta a nan Libya.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel