Buhari ya yi korafi a kan yawan yajin aikin malaman jami'o'i

Buhari ya yi korafi a kan yawan yajin aikin malaman jami'o'i

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi korafi a kan yawan yajin aiki da kungiyoyin malaman jami'o'i su keyi inda ya ce hakan na matukar kawo cikas ga tsarin ilimi na kasar.

Ya yi wannan korafin ne a taron yaye dalibai na karo 35, 36 da 37 da aka hada na Jami'ar Usamanu Danfodio a Sokoto a ranar Asabar.

Shugaba Buhari, wanda Karamin Ministan Ilimi, Farfesa Anthony Anwukah ya wakilta ya roki kungiyoyin su rika yiwa gwamnati uzuri saboda tana sane da matsalolin da suke fama da shi kuma ba za tayi kasa a gwiwa ba har sai da warware su.

Buhari ya yi korafi a kan yawan yajin aikin malaman jami'o'i

Buhari ya yi korafi a kan yawan yajin aikin malaman jami'o'i
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Ya ce yajin aikin yana kawo cikas da karatun dalibai da kuma samar da wadanda za suyi ayyuka a kasar.

A cewar shugaban kasar, gwamnatinsa ta fara ganin amfanin kudaden da ta ke sanya wa a fannin ilimin.

Duk da haka, ya bukaci mahukunta jami'o'in su bullo da hanyoyin inganta jin dadi da walwalan ma'aikatansu da dalibansu.

A yayin da ya ke taya wadanda suka kammala karatun su murna, ya kuma horre su da su kasance wakilai na gari ga jami'ar da kasar baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel