Zaben 2019: Sakamakonka na yanar gizo jabu ne - INEC ta fadawa Atiku

Zaben 2019: Sakamakonka na yanar gizo jabu ne - INEC ta fadawa Atiku

-Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta karyata Atiku Abubakar akan sakamakon zabe na bogi

-Atiku Abubakar ya samo sakamakon da yake nuna cewa shine ya lashe zaben 2019 ba Buhari ba inda bai yi wata-wata ba ya mika shi a gaban kotu matsayin shaida.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta zargi Atiku Abubakar da kirkirar sakamako na bogi domin ya bada shi a matsayin hujja gaban kotun sauraren korefe-korefen zabe. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, hukamar ta zabe ta mayar da martani akan wannan lamari zuwa ga kotun dake Abuja ranar Alhamis.

Bugu da kari, jaridar ta cigaba da cewa, hukumar ta INEC ta nisanta kanta daga duk wani sakamako dake kunshe a shafin yanar gizo. Ga kuma abinda take cewa, “Bamu kasance muna sakin sakamakon zabe akan yanar gizo ba, a don haka duk wani sakamako da aka samu akan shafin ba sahihi bane.”

Shugaban hukumar zabe

Mahmood Yakubu
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Faduwa zabe ba kanka aka fara ba, Gwamnatin tarayya ta fadawa Atiku

Har wa yau, “INEC ta karyata duk wani labarin cewa ta kasance tana sanya sakamakon zabe a kan yanar gizo, bal ma tace yin hakan saba ma dokokin tsarin zabe ne ‘Electoral Act’ na shekarar 2010, kamar yanda akayi garanbawul.

A watan jiya ne tawagar lauyoyin Atiku suka shigar da wannan kara inda suka baiwa kotun takardar dake dauke da wannan sakamakon, suna masu cewa an samu sakamakon ne daga shafin hukumar INEC na yanar gizo a bangaren da suke tara sakamakon zabuka.

Haka zalika, yayinda tawagar ke mika wannan shaidar sun fadi cewa, Atiku shine ya lashe zaben da tazarar kuri’a sama da miliyan shida amma sai dai hukumar zaben tayi irin nata munakisar ta juya sakamakon kana aka baiwa Shugaba Buhari cewa shine dan takarar da yayi nasara a wannan zabe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel