Yanzu-yanzu: Buhari ya sauka a kasar Chadi

Yanzu-yanzu: Buhari ya sauka a kasar Chadi

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin N'Djamena babban birnin kasar Chadi a yau Asabar 13 ga watan Afrilun 2019 domin hallartar taron shugabani kasashen nahiyar Afrika da ke yankin Sahel Sahara, CEN-SAD.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN ta ruwaito cewa jirgin shugaban kasar da tawagarsa ciki har da wasu gwamnoni uku sun sauka a filin tashi da saukan jirage na Hassan Djamous International Airport N’Djamena misalin karfe 9.40 na safe.

Wadanda suka tarbi shugaban kasar da tawagarsa sun hada da Ministan Harkokin Kasashen Waje, Mr Geoffrey Onyaema da Janar Abdulrahman Dambazau mai murabus.

Yanzu-yanzu: Buhari ya sauka a kasar Chadi

Yanzu-yanzu: Buhari ya sauka a kasar Chadi
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Khadimul islam: Ganduje ya rufe wani babban Otel a Kano, an kama masu karuwanci 19

Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Brig. Janar Mansur Dan Ali; Mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Babagana Monguno da Mr Nasiru Waje.

Buhari da sauran shugabani za su hadu da mai masaukin bakinsu kuma shugaban CEN-SAD, Shugaba Idriss Deby Itno domin tattaunawa a kan harkokin siyasa da tsaro da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel