Dalilin da yasa baza a iya kawar da sayen kuri’a ba, inji Farfesa Munzali

Dalilin da yasa baza a iya kawar da sayen kuri’a ba, inji Farfesa Munzali

- Sayen kuri'u ya kasance daya daga cikin matsolin dake kawa cikas lokacin manyan zabuka a kasar nan.

- Dole gwamnati ta tashi tsaye domin magance matsalolin da suka shafi tsaro a kasar nan.

Tsohon babban Sakataren Hukumar kula da Jami’o’i ta kasa wato NUC kuma mataimakin shugaban Jami’ar gwamnatin tarayya dake Lafia a jihar Nasarawa, Farfesa Munzali Jibril ya fadi ra’ayinsa dangane da zaben 2019 da kuma matsalolin tsaron dake addabar kasar nan a halin yanzu yayinda yake zantawa da yan jarida. Ga kuma yanda tattaunawar ta kasance:

Yan jarida: Shin me zaka iya cewa game da zaben 2019?

Farfesa Munzali Jibril: A nawa ganin dai an gudanar da zabukkan lami lafiya. Duk da cewa yan wasu Najeriya sunyita korefe-korefe akan rashin kammaluwar wasu daga cikin zabukan, sai dai ni ina kallon abin ne da wata mahanga ta daban.

Tsananin ingancin zaben ne ya haifar da samun cewa wasu daga cikin zabukan da akayi sakamakonsu bai kammala ba sabanin yanda mutanen kasa ke ganin hakan a matsayin wata gazawace daga wurin hukumar zabe mai zaman kanta. Sam ni ban aminta da wannan batu ba.

Har wa yau, na fahimci cewa zaben kasar nan ya dauki sabon salo ganin cewa da can, ba asalin abinda jama’a suka zaba ake basu ba. Saboda a da can zaka ga masu zaben dan takarar shugaban kasa na wata jam’iya sai kaga idan aka zo zaben gwamna sakamakon ya sha bambam da ita waccan jam’iyar duk kuma a wuri guda.

Farfesa Munzali

Farfesa Munzali
Source: UGC

KU KARANTA:Abba ya shigar da Ganduje kara kotu bisa nasarar da ya samu

Wannan abu yana matukar rikitar da jama’a. Naji wasu na fadin cewa wai an tafka magudi a zaben shugaban kasa, to idan ba magudi ba ya za ayi a kuri’un da gwamna ya samu su sha bambam da wanda shugaban kasa ya samu. Duba ga hakan ko shakka babu wannan kawai, ka iya cewa tunanine na jama’a daban daban wanda kowa na iya fadin abinda ya ga dama. A gani na dai an gudanar da zabe cikin lumana amma dai ba’ a rasa yan kura-kurai ba wanda za’a gyara ko dan gaba.

Yan siyasan Najeriya na da dubara kwarai da gaske, saboda duk da irin na’urorin zamani na fasaha da hukamar INEC take dasu amma hakan bai iya hana magudin zaben ba a wurare da dama.

Yan jarida: Kace zaben yayi kyau, amma sai dai matsalar sayen kuri’u dake yawo kusan a ko ina. Me zakace game da wannan matsalar duk da cewa akwai kasancewar jami’an tsaro da dama?

Farfesa Munzali: Ko shakka babu sayen kuri’a babbar matsalace. Kuma gaskiya ba zan iya ce maka ga hanyar da za abi domin magance wannan matsala ba sai dai yanda za a rage yaduwar hakan a hankali. Bari in baka wani labari, lokacin da na koma gida can Kano, domin yin zabe nayi ta ganin mutane masu sayen kuri’a amma kai idan ka gansu ba zaka ganesu ba. Nesa suke tsayawa ba wai cikin jama’a da sun hangenka tafe sai su matso kusa suna cewa, ni ina wakiltar jam’iya kazane zan baka naira dari biyu ko dari biyar ka zabi jam’iyarmu.

Idan kuwa ka shiga ganawa da masu zaben sai kaji suna ce maka; ai duk ma wanda ka zaba ba wani abun zai tsinana maka ba har tsawon shekaru hudunsa, kai har gwara ma ka amshi dari biyun ko dari biyar ko ta toshe maka wata kafar a yanzu. Wannan abu yana faruwane nesa da wajen da ake jefa kuri’a.

A takaice dai talauci ne ya wa mutane yawa da har yasa su siyar da 'yancinsu akan wasu yan kudi kalilan. Inda ace za ayi tunanin hanyoyin karfafa jama’a domin a rage talauci to da hakan ya taimaka kwarai da gaske wajen yaye wannan matsala. Domin abin ya fara zarce tunanin mutane inda wasu lokutan da mota ake zuwa cike da kudi sai a bude a kira masu kada kuri’a domin a sayesu su zabi ita wannan jam’iyar ba wai don suna so ba sai dan kudin da aka basu. Kai wani lokacin ma har tura yan sanda ake domin su binciki irin wannan badakkala amma sai su ki zuwa.

Yan jarida: An samu barkewar rikici a jihohin Kano, Ribas da ma wasu wurare da dama duk da jajirtaccen shirin da akayi. Shin babu abinda za' a iya yi domin kawo karshen rikicin zabe da wasu matsalolin da suka hada da magudin zaben ne?

Farfesa Munzali: Faruwar wannan abu ya girgiza ni matuka. Wannan abu yana faruwa ne sakamakon yan siyasar da suke kan mulki kana kuma suke hango faduwarsu daf dasu. Dalilin hakan ne yasa zasu iyayin komi domin su ga cewa sun koma bisa kujerar tasu. Jami’an tsaro kuma a nasu bangaren bai kamata su nuna goyon baya ga kowace jam’iya ba domin haka shine zai basu daman kama duk wani mai tayar da irin wannan fitina.

Yan jarida: A bangaren tsaro, banda rikicin manoma da makiyaya, akwai matsalar garkuwa da mutane wadda ta zama ruwan dare a yau. Shin hakan kuwa ba nakasu bane musamman ga gwamnatin da samar da tsaro na daga cikin manyan kudorinta guda hudu?

Farfesa Munzali: Hakika wannan babban kalubale ne ga gwamnatin nan. Muna da bukatar kaifin tunani da kuma shiri na musamman domin kawo karshen wannan matsalar. A nawa ganin abu ne mai yiwuwa a mangance matsalar nan cikin makonni ko wasu yan watanni sai dai hakan zai yi matukar wuya. Duba da cewa matsalar garkuwa da mutane kawai a kasarnan ta addabi mutane saboda masu aikata wannan laifin da sunyi so daya suka sam kudi sai kuma su cigaba dayi.

Idan ka dubi hanyar Kaduna zuwa Abuja da ake yawan sace mutane, ai tun daga Zamfara suke bibiyar matafiya saboda sun shahara kwarai wajen gudunar da wannan ta’asa. A halin yanzu kuwa ita kanta Zamfara ta zama matattarar sace mutane ba dare ba rana. Amma dai idan za ayi amfani da dubarar aikin tsaro gwamnati zata iya samun duk labaran da za suyi mata amfani wajen dakatar da wannan ta’addanci. A wani lokacin ma za kaga ko da a ce an sanar da jami’an tsaro an sace wasu mutane can kuma ba da dadewa ba sai kaji an sako su, har ma su iya rako mutanen kimanin mita dari daga madakatar da yan sanda ke tsayuwa a bisa titi, har ma su ce dasu idan yan sanda sun tambeyaku ku ce dasu mune muka sauke ku yanzun nan.

Daga jin haka sun kuma yan sandan zasu shiga neman wadannan masu garkuwa da mutane bukatarsu kawai suji, nawa ne aka biyasu kafin su saki wadannan mutane, domin suma a basu wani abu cikin kudin. Wannan dalilin ne yasa yinkuri na farko da akayi wajen yaki da masu garkuwa da mutane, aka sauya jami’an yan sandan dake tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja aka kawo sabbi. Ya zama tilas ga gwamnati da ta sake zage dantse kwarai da gaske.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel