Shugaban sojin da ya kwaci mulki a Sudan ya ajiye mukamin sa

Shugaban sojin da ya kwaci mulki a Sudan ya ajiye mukamin sa

Ministan tsaron kasar Sudan Awad Ibn Auf ya bayyana ajiye mukaminsa na shugaban kasar Sudan, bayan kwana daya da yin juyin mulki a kasar. Sannan ya bayyana Laftanal Janar Abdel Fatah Abdulrahman Burhan a matsayin wanda zai hau kujerar ta shi.

Ministan ya bayyana kudurin na sa ne a wani gidan talabijin na gwamnatin kasar ta Sudan.

Matakin da ministan ya dauka ya biyo bayan kin amincewa da 'yan zanga-zangar kasar suke nunawa, inda suke nuna rashin amincewarsu da sababbin shugabannin sojin da suka hau mulkin kasar, 'yan zanga-zangar su na zargin shugabannin da hannu cikin matsalar tsaro da ta addabi kasar ta Sudan.

Shugaban sojin da ya kwaci mulki a Sudan ya ajiye mukamin sa

Shugaban sojin da ya kwaci mulki a Sudan ya ajiye mukamin sa
Source: UGC

Sojojin da suka hambarar da mulkin sunyi alkawarin gabatar da zabe sannan kuma su mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekaru 2 masu zuwa.

Tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir ya rasa kujerarsa ne bayan da aka dauki lokaci mai tsawo ana zanga-zanga a kasar ta nuna kiyayya karara ga mulkinsa. Ta dalilin zanga-zangar ya sanya aka yi asarar rayukan mutane kimanin 38 a kasar.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Ministan tsaro Awad ibn Auf ya taba rike mukamin shugaban sojoji 'yan leken asiri na cikin gida a lokacin da aka yi yakin Darfur a shekarar 2000, sannan kasar Amurka ta yi masa takunkumi a shekarar 2007.

Kotun manyan laifuka ta duniya ta kama tsohon kasar Al-Bashir da laifin cin zarafin al'ummar kasar da kuma tada zaune tsaye, a dalilin wancan yaki da aka yi na Dafur.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel