Sai na yi nazari kafin na karbi mukami a hannun shugaba Buhari - Dan takarar shugaban kasa

Sai na yi nazari kafin na karbi mukami a hannun shugaba Buhari - Dan takarar shugaban kasa

- Dan takarar shugaban kasa da ya fito a jam'iyyar YPP ya bayyana kudurin sa na ajiye siyasa a kasar nan

- Sannan kuma ya bayyanacewa koda Buhari zai ba shi mukami sai ya yi nazari sosai kafin ya karba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar YPP, Kingsley Moghalu, wanda ya fito aka gwabza dashi a zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairun da ya gabata ya ce ko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi mukami a gwamnatinsa ba zai yi saurin karba ba har sai ya yi tunani akai.

Bayan haka kuma Moghalu ya bayyana kudurin shi na janyewa daga siyasar kasar nan.

Moghalu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jiya Juma'a a Abuja.

A lokacin da ya ke bayyana abinda ya sa gaba, Moghalu ya ce yanzu zai maida kai ne wurin kawo cigaba a harkar siyasar kasar nan.

Sai na yi nazari kafin na karbi mukami a hannun shugaba Buhari - Dan takarar shugaban kasa
Sai na yi nazari kafin na karbi mukami a hannun shugaba Buhari - Dan takarar shugaban kasa
Source: UGC

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriyan (CBN) ya ce: "Na yi kudurin janyewa daga harkar siyasar kasar nan a yanzu.

"Za mu maida kai wurin kawo cigaba a harkar siyasa tare da wayar da kan al'umma ta hanyar koya musu yadda siyasa ta ke.

"Wadannan su ne abubuwan da siyasar kasar nan ta ke bukata idan har ana son cigaba a fannin siyasa."

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Da aka tambayeshi ko zai karbi mukami idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi a gwamnatinsa, sai ya ce: "Idan har hakan ta faru zanyi tunani ne farko kafin na yanke hukunci akan karbar mukamin."

Dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar YPP ya zo na 14 a jerin wadanda suka fito takarar, da kuri'u 21,886 a zaben da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel