Majalisa ba matattaran 'yan boko bane - Dogara ga zababun 'yan majalisa

Majalisa ba matattaran 'yan boko bane - Dogara ga zababun 'yan majalisa

Kakakin majalisar wakilan dokoki na tarayya, Mr Yakubu Dogara ya shawarci sabbin zababun 'yan majalisar da kada suyi tsamanin majalisar matattara ce ta 'yan Boko.

Ya ce su dauki kansu a matsayin wakilan al'ummarsu kuma kada su manta da dalilin da yasa aka zabe su musamman kallubalen tsaro, rashin ayyukan yi da talauci da fatara da al'umma ke fama da ita.

Sanarwar da ofishinsa ta fitar a ranar Juma'a ya ce Kakakin majalisar ya yi wannan jawabin ne a daren Alhamis a wurin wata liyafar cin aminci da aka shirya domin yin maraba da sabbin zababun 'yan majalisa.

Majalisa ba matattaran 'yan boko bane - Dogara ga zababun 'yan majalisa

Majalisa ba matattaran 'yan boko bane - Dogara ga zababun 'yan majalisa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Khadimul islam: Ganduje ya rufe wani babban Otel a Kano, an kama masu karuwanci 19

"Ina son in tunatar da mu cewa bayan wannan taron za muyi rantsuwar fara aiki. Saboda haka bai kamata mu rudi kan mu ba kamar da cewa mun shiga wata kungiyar wasu 'yan boko ne a kasar nan. Hasali dai mu wakilan al'umma ne masu wakiltan mutanen mu," inji shi.

"Ba zai yiwa mu bawa al'ummar da suka zabe mu kunya ba. Abinda kawai muke bukata domin kawo canji shine ilimi. Idan muna aiki da ilimi za mu iya gudanar da ayyukan mu kuma muyi nasara."

"A matsayin mu na wakilan al'umma ba zai yiwu muyi barci ba a irin wannan lokacin da al'ummar mu ke cikin mawuyacin hali na rashin tsaro, rashin ayyukan yi da sauransu."

Ya kara da cewa da zarar sun kama aiki akwai yiwuwar abubuwa za suyi musu yawa amma ya tunatar da su cewa aikinsu shine kawo karshen wahalhalun da 'yan Najeriya ke ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel